A karo na hudu, gobara ta yi kaca-kaca da shararriyar kasuwa a Abuja

A karo na hudu, gobara ta yi kaca-kaca da shararriyar kasuwa a Abuja

  • Wata mummunar gobara ta tashi a Abuja, inda ta lalata dukiyoyi a shahararriyar kasuwar nan ta Karimo
  • Zuwa yanzu ba a san me ya haddasa gobarar ba wacce ta fara ci daga wani shago a safiyar Alhamis, 31 ga watan Maris
  • Yan kasuwa na ci gaba da kirga asarar da suka yi yayin da suke tsiratar da sauran kayayyakin da basu kone ba

Abuja - Gobara ta tashi a shahararriyar kasuwar nan ta babbar birnin tarayya da ke Karimo a safiyar yau Alhamis, 31 ga watan Maris.

Bincike sun nuna cewa har yanzu ba a san musababbin tashin gobarar ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Da dumi-dumi: Gobara ta sake tashi a kasuwar Karimo da ke birnin Abuja
Da dumi-dumi: Gobara ta sake tashi a kasuwar Karimo da ke birnin Abuja Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Wani dan kasuwa mai suna Sunday ya fada ma jaridar cewa annobar ta fara ne daga wani shago kafin daga baya ta yadu zuwa sauran wurare.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Birtaniya Ta Gargaɗi Ƴan Kasarta Game Da Ziyartar Jihohin Arewa 7 a Najeriya

Wannan shine karo na hudu da kasuwar Karimo ke tashi da gobara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sunday ya ce:

“Yan kasuwa sun fara kirga asarar da suka yi tare da ceton sauran kayayyakin da suka rage masu.

Kayayyakin miliyoyin naira sun halaka a annobar, a cewar yan kasuwa.

Innalillahi: Wata gobara ta sake barkewa, ta yi kaca-kaca da gidaje a jihar Legas

A wani labarin, mun ji a baya cewa sa’o’i kadan bayan wata gobara da ta tashi ta lalata kayyakin miliyoyin Naira a kasuwar Apongbo da ke tsibirin Legas, an sake samun barkewar wata gobarar a yankin Marine Beach da ke Apapa a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, gobarar ta biyu ta lalata wasu kananan gidajen kwana a yankin.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 12:45 na rana, kamar yadda wasu masu aikin ceto a yankin suka bayyana.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka jama'a masu yawa a sabon harin da suka kai Benue

Asali: Legit.ng

Online view pixel