Shugaban matasan APC da wani babban jigo sun yi hatsari, Allah ya musu rasuwa

Shugaban matasan APC da wani babban jigo sun yi hatsari, Allah ya musu rasuwa

  • Allah ya yi wa shugaban matasan APC rasuwa da wani mamba da suke tare sanadiyyar hatsarin Mota a jihar Oyo
  • Rahoto ya nuna cewa mutanen biyu na cikin Mota a kan hanyarsu ta komawa gida wata Tirela ta dakon siminti ta niƙe su
  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra FRSC ta Oyo, ya ce ɗayan su ya rasu nan take, yayin da ɗayan ya cika a Asibiti

Oyo - Shugaban matasan APC na ƙaramar hukumar Ogbomoso North a jihar Oyo, Afolabi Tunde, da wani mamba mai suna Sabitu, sun yi hatsari a yankin Ogbomoso.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata Tirela ta dakon Siminti ce ta bugi motarsu shugaban matasa a tashar Caretaker bus stop, Ogbomoso.

Bayanai sun nuna cewa Tunde, wanda ɗaya ne daga cikin Deleget daga jihar Oyo a babban taron APC da aka kammala, bai jima da murnar cika shekara 49 ba.

Kara karanta wannan

Yadda zan jagoranci jam'iyyar APC ta samu nasara a 2023. Sanata Adamu ya magantu

Tutar jam'iyyar APC.
Shugaban matasan APC da wani babban jigo sun yi hatsari, Allah ya musu rasuwa Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Wani shaidan da akai abun a gabansa ya ce Tirelar ta niƙa mutanen ne yayin da suke cikin Mota a kan hanyarsu ta komawa gida.

Shugaban matasan APCn ya rasa rayuwarsa ne nan take a wurin da lamarin ya faru, yayin da Sabitu kuma ya rasu a Asibiti.

Hukumar FRSC ta tabbatar da aukuwar lamarin

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa, (FRSC) reshen jihar Oyo, Uche Chukwurah, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma mutuwar mutanen biyu.

A kalamansa, Kwamandan FRSC ya ce:

"Ɗaya daga cikin waɗan da hatsarin ya rutsa da su ya rasa rayuwarsa ne nan take a wurin da lamarin ya faru, yayin da ɗayan kuma ya kwanta dama bayan an kai shi Asibiti."
"Zamu cigaba da ilimantar da masu amfani da hanyoyin ƙasar nan bukatar dake akwai na yin tuƙi cikin natsuwa da kula."

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: An fara gano yawan mutanen da suka mutu a harin jirgin ƙasan Kaduna

A wani labarin na daban kuma Mutanen Gombe sun kai ƙarar Pantami Kotu kan neman takarar gwamna a zaɓen 2023

Wasu tawagar mutane a jihar Gombe sun maka Ministan Sadarwa, Isa Pantami a gaban Kotu kan kujerar gwamna.

Shugaban ƙungiyar mutanen ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne domin tilasta masa ya nemi takarar gwamna a Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel