Jami'an hukumar EFCC Sun Cafke wani Kasurgumi ɗan Najeriya da Amurka ke nema ruwa a Jallo

Jami'an hukumar EFCC Sun Cafke wani Kasurgumi ɗan Najeriya da Amurka ke nema ruwa a Jallo

  • Hukumar EFCC ta samu nasarar kama wani ɗan Najeriya da FBI ta ƙasar Amurka ke nema ruwa a jalllo
  • Jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta'adi sun yi ram da mutumin ne a karamar hukumar Orlu ta jihar Enugu
  • FBI na zargin mutumin mai suna, Emmanuel Dike Chidiebere, da aikata damfara da halasta kuɗin haram a ƙasashen uku

Abuja - Wani ɗan Najeriya dake cikin jerin mutanen da hukumar bincike ta ƙasar Amurka (FBI) ke nema ya shiga hannu a Orlu, jihar Enugu, kamar yadda Punch ta rahoto.

Shiyyar hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annadi ta ƙasa (EFCC) ta jihar Enugu ce ta cafke mutumin, a cewar wata sanarwa.

Hukumar EFCC ta kama ɗan damfara a Najeriya.
Jami'an hukumar EFCC Sun Cafke wani Kasurgumi ɗan Najeriya da Amurka ke nema ruwa a Jallo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, FBI na neman ɗan Najeriyan ruwa a jallo ne bisa zargin haɗa kai, damfarar Intanet da kuma halasta kuɗin haram.

Kara karanta wannan

Matasa sun fara lalata filin kwallon Abuja sakamakon kashin da Najeriya ta sha hannun Ghana

Premium Times ta rahoto Sanarwan da EFCC ta fitar ta ce:

"EFCC ta kama wani mutumi da FBI ke nema ruwa a jallo. Hukumar ta shiyyar Enugu ta damƙe, Emmanuel Dike Chidiebere, a Enugu, wanda FBI ke zargi da haɗa baki, damfarar Intanet da halasta kuɗin haram."
"Bayan samun bayanan sirri, dakarun EFCC a ranar 23 ga watan Maris, 2022 suka bibiyi maɓoyar wanda ake zargin har ƙaramar hukumar Orlu, inda suka cafke shi."
"Ana zargin Chidiebere da damfarar wasu mutane a Amurka, Cote D’Ivoire da kuma Poland adadi mai yawa na kuɗaɗe da ba'a bayyana ba kuma ya yi ɓatan dabo. Har yanzun akwai sauran mutum uku da suke taimaka masa da ake nema."

A wani labarin na daban kuma Mutanen Gombe sun kai ƙarar Pantami Kotu kan neman takarar gwamna a zaɓen 2023

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe wani Dirakta a hukumar NBTE, yana cikin jirgin kasa Abuja-Kaduna

Wasu tawagar mutane a jihar Gombe sun maka Ministan Sadarwa, Isa Pantami a gaban Kotu kan kujerar gwamna.

Shugaban ƙungiyar mutanen ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne domin tilasta masa ya nemi takarar gwamna a Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel