Kotu Ta Yanke Wa Wata Mata Hukunci Saboda Taimakawa Ɗanta Aikata Damfarar Intanet

Kotu Ta Yanke Wa Wata Mata Hukunci Saboda Taimakawa Ɗanta Aikata Damfarar Intanet

  • Wata kotun tarayya da ke zamanta a Benin City, ta samu wata mata da laifin taimakawa danta wurin aikata laifin damfarar kudi ta intanet
  • Kotun ta samu Debest Osarumwense ne da laifin karbar zunzurutun kudi Naira miliyan 9.1 duk da ta san kudin damfara ne da danta ya aikata
  • Matar, Osarumwense, ta amsa laifin da ake tuhumarta daga nan alkalin kotun ya yanke mata hukuncin daurin shekara 5 a gidan yari amma da zabin biyan tara

Jihar Edo - Babban kotun tarayya da ke Benin City, Jihar Edo, ta yanke wa wata mata Debest Osarumwense hukunci, saboda taimakawa danta da ake zargi da aikata damfarar intanet.

Alkalin kotun, M.S. Shuaibu, a hukuncinsa, ya samu matar da laifin taimakawa danta, Endurance Osarumwense, wurin karbar kudi Naira miliyan 9.1 na damfarar intanet, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Muna alfahari: Gwamnatin Buhari ta ji dadin yadda 'yan Najeriya ke more tafiya a jirgin kasa

Kotu Ta Yanke Wa Wata Mata Hukunci Saboda Taimakawa Ɗanta Aikata Damfarar Intanet
Kotu Ta Yanke Wa Wata Mahaifiya Hukunci Saboda Taimakawa Ɗanta Aikata Damfarar Intanet. Hoto: The Nation.

Kotu ta yanke wa Osarumwense hukuncin daurin shekaru 5 da zabin biyan naira miliyan 1

Mrs Shu'aibu ta yankewa matar daurin shekaru biyar tare da zabin tarar Naira miliyan 1, kakakin hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Uwujaren ya ce Mrs Osarumwense ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi.

Bayan amsa laifinta, lauya mai gabatar da kara, I.K. Agwai, ya roki kotun ta tabbatar da laifinta sannan a yanke mata hukunci.

A hukuncinta, alkalin kotun ta yanke mata daurin shekaru biyar a gidan gyaran hali amma da zabin biyan tara, an kuma umurci ta mika sauran kudaden da ke asusunta ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Ga tuhumar da aka karanto mata:

"Ke, Debest Osarumwense, wani lokaci tsakanin 2 zuwa watan Janairu da Disamban 2021 a Jihar Edo inda kotun nan ke da iko kun karbi kudi N91,296,150.00 duk da cewa kin san kudi ne da Endurance Osarumwense (dan ki) ya samu ta hanyar aikata damfarar intanet wanda laifi ne a karkashin sashi 17(b) na dokar EFCC ta Act 2004."

Kara karanta wannan

Ya cika burinsa: Labarin tsohon da ya samu takardar kammala sakandare yana da shekaru 101

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

A wani labarin, an kama wani mai aiki a wurin wankin mota a Kano, Abdullahi Sabo, saboda tsere wa da motar kwastoma da aka kawo masa wanki, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Daura, Jihar Katsina da motar na sata.

Mr Kiyawa ya ce, a ranar 30 ga watan Nuwamba, yan sanda sun samu korafi daga wata mazauniyar Badawa Quaters a Kano inda ta ce wani mai aiki a wurin wankin mota ya gudu masa da motarsa Honda Accord ta shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel