Hutu Hameed Ali ya tafi, baya cikin halin rashin lafiya, inji hukumar Kwastam

Hutu Hameed Ali ya tafi, baya cikin halin rashin lafiya, inji hukumar Kwastam

  • Hukumar kwastam ta yi watsi da rahoton da ke yawo cewa shugabanta, Hameed Ali ya yanke jiki ya fadi
  • Ta kuma bayyana cewa kanzon kurege ne cewa an kwashi shugaban nata zuwa waje domin yin jinya
  • Kakakin hukumar, Timi Bomodi, ya ce ubangidan nasu na cikin koshin lafiya illa kawai ya tafi hutu ne

Hukumar kwastam na Najeriya, ta karyata rahoton kafar yada labarai da ke cewa shugabanta, Hameed Ali ya yanke jiki ya fadi a ranar Laraba sannan cewa an fitar da shi kasar waje don jinya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Maris, dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kwatsam, mataimakin kwanturola, Timi Bomodi, Daily Nigerian ta rahoto.

Hutu Hameed Ali ya tafi, baya cikin halin rashin lafiya, inji hukumar Kwastam
Hutu Hameed Ali ya tafi, baya cikin halin rashin lafiya, inji hukumar Kwastam Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya bayyana cewa rahoton kanzon kurege ne, domin Ali yana cikin koshin lafiya sannan ya tafi hutu ne.

Kara karanta wannan

Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari

Premium Times ta nakalto sanarwar yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An ja hankalin hukumar NCS zuwa ga wani rahoton yanar gizo da ke cewa kwanturola janar na Kwastam ya yanke jiki ya fadi sannan cewa an fitar da shi kasar waje domin jinya.

“Domin tsokaci kai tsaye kan lamarin, Ali na cikin koshin lafiya kuma baya rashin lafiya kamar yadda wata kafar labarai ta yanar gizo da ba a ambaci sunanta ba ta rahoto.

“Kwanturola janar din wanda a tsawon wa’adin shugabancinsa ya sadaukar da lokacinsa da karfinsa domin gyara manufar wannan gwamnati ta samu tarin nasarori wajen sake fasali da tara kudaden shiga masu tarin yawa da ba a taba samun irin su ba.

“Mun san cewa wasu mutane na kokarin amfani da damar tafiyarsa hutu wajen haddasa cece-kuce mara tushe.

“Wannan ba zai janye hankalin hukumar NCS daga aiwatar da aikinta ba yayin da take kokarin sake gina wata cibiya mai daraja ta duniya wacce ta cancanci addu'a da goyon bayan dukkan 'yan Najeriya.”

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Mista Bomodi ya sake ba dukka masu ruwa da tsaki da yan Najeriya masu daraja tabbacin cewa kwanturola janar din na cikin koshin lafiya, yana mai gargadin cewa za a dauki mataki na doka ga masu yada labarin karya.

Jerin abubuwa 8 da Hukumar Kwastam ta hana fitar da su zuwa kasashen waje

A wani labarin, hukumar kwastam ta Najeriya ta bayyana jerin abubuwa da kayayyaki da aka haramta fitar da su daga kasar.

Duk wani yunkuri na fitar da wadannan kayayyaki da aka ambata a fadin iyakokin kasar zai zama wanda baya bisa ka’ida kuma za a hukunta mutum a karkashin dokokin kasar da suka dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel