Tashin hankali: Bidiyon yadda mata ta shekara tana tara kudi a asusu, ta ga N90 yagaggu

Tashin hankali: Bidiyon yadda mata ta shekara tana tara kudi a asusu, ta ga N90 yagaggu

  • Wata 'yar Najeriya ta koka kan bukatar mutane su samu amintaccen mai sayar da asusu kafin su sayi inda za su adana kudadensu
  • Matar ta yi wannan b ayani ne sakamakon wani abin ban mamaki da ya faru da ita bayan ta fasa asusunta kuma ta samu N90 a ciki
  • A cewar matar, ta kwashe sama da shekara guda tana saka N300 a kowace rana kuma tana sa ran samun akalla dai ko N100k ne

Wata ‘yar Najeriya ta shiga rudani bayan da ta fasa asusunta na katako sai kawai ta ga N90 kacal a ciki.

Wani dan gajeren bidiyo da @krakshq ya yada a Instagram ya nuna lokacin da matar ta fasa dan karamin akwatin na katako da tabarya.

Yadda mata ta yi wa aljanu asusu
Tashin hankali: Bidiyon yadda mata ta shekara tana tara kudi a asusu, ta samu N90 yagaggu | Hoto: @krakstv
Asali: Instagram

Bayan ta yi nasarar fasa shi, sai ta bude don ganin meke ciki, sai ta cika da mamaki ganin yagaggun kudi N90 kacal.

Matar da ke cikin rudani ta bayyana cewa ta yi tsammanin samun kusan N100k domin ita da ‘yar uwarta sun kwashe sama da shekara guda suna saka Naira 300 a kowace rana a asusun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta fada cikin mamakin yadda wannan abu ya kasance.

Matar ta ci gaba da ba mutane shawara kan su kula da inda suke sayen asusun katako a wannan zamani, domin kuwa duniya ba yarda.

Ra'ayoyin 'yan soshiyal midiya

@feg_ggy ya ce:

"Wani ne a zahiri yake dauke kudin, kanwata ta yi min haka bara, da zarar na aje kudi amciki sai ta cire har dai na kama ta."

@uche_creative ya ce:

"'Yar uwa don ALlah ki tambayi 'yan uwanki maza kan meye faru da wadancan kudi saboda banson rashin hankali domin nasan yadda ni da kanwata muka sha fama da irin wannan."

@omoakin ya ce:

Ba abinda kika ajiye za ki gani ba, ko dai baki tuna lokacin da kike amfani da kudinki wajen cin shawarma ba, Coldstone sannan kice komai zai mike, dole 'yan siddabaru su dauki kudin aikinsu, karki manta haka.

Ajiya maganin watarana: Dan Najeriya ya fasa asusunsa, kudin da ya tara sun girgiza intanet

A wani labarin, ya zuwa yanzu dai, wani dan Najeriya ya fasa asusunsa don gane wa idonsa makudan kudaden da ya tara a ciki. Ko da yake bai bayyana lokacin da ya fara tara kudin ba, wani faifan bidiyo ya nuna mutumin yana kirga kudinsa masu daraja daban-daban.

Kokarin da mutumin ya yi na tara wani kaso daga kudinsa na shiga saboda ya mora a nan gaba ya ja hankalin jama'a a shafukan sada zumunta. Mutane da yawa sun yaba masa saboda kokarin da ya yi ganin yadda ake fama da babu a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel