Zaben Shugabanni: APC ta bayyana abubuwan da za a zo dasu filin taron gangami

Zaben Shugabanni: APC ta bayyana abubuwan da za a zo dasu filin taron gangami

  • Jam’iyyar APC mai mulki, ta bayyana sharadan da ta gindaya wa wakilan jam'iyya gabanin zaben fidda gwani da za a yi
  • Alhaji Tijjani Musa Tumsah, sakataren kwamitin karramawa ne ya bayyana haka a kafafen sada zumunta na zamani.
  • A cewarsa, dole ne wakilan da za su kada kuri'a a zaben da za a yi su zo da katin tantancewa ko nuna shaida

Gabanin taron gangamin jam’iyyar APC na kasa, jam’iyyar ta bayyana cewa ya zama wajibi wakilan da za su kada kuri'a a zaben da za a yi a taron su zo da shaidar tantance su.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne ta bakin sakatarenta na kwamitin karramawa Alhaji Tijjani Musa Tumsah ne a dandalin sada zumunta.

Abubuwan da wakilai za su zo dashi taron gangamin APC
Zaben Shugabanni: APC ta bayyana abubuwan da za a zo dasu filin taron gangami | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A sanarwar da ya fitar, wani bangare ya ce:

Kara karanta wannan

Zaben APC: An fitar da sabuwar sanarwa, masu rike da mukamai ba za su yi zabe ba

"Ana kira ga dukkan wakilan da za su halarci taron gangami na kasa na ranar 26 ga Maris, 2022 da su zo tare da katin shaida da gwamnati ta amince dashi."

Bayan wannan batu na sama ne jam'iyyar ta bayyana nau'in katin da za a iya zuwa dashi kamar haka:

1. Lasisin tuki na hukumar FRSC

2. Katin zabe na dindindin

3. Fasfo na kasa da kasa

4. Katin shaidar zama dan kasa

Idan baku manta ba, rahotannin da muka kawo muku a baya sun bayyana yadda jam'iyyar APC ta dukufa wajen gudanar da taronta na gangami.

Jam'iyyar ta shirya gudanar da taron gangamin ne a gobe Asabar, 26 ga watan Maris 2022, inda za a zabi sabbin shugabannin jam'iyyar.

Kadan kenan daga cikin shirye-shiryen jam'iyyun siyasan kasar nan gabanin babban zabe da zai gudana a 2023.

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

Zaben APC: An fitar da sabuwar sanarwa, masu rike da mukamai ba za su yi zabe ba

A wani labarin, jam’iyyar APC mai mulki ba za ta bar wadanda suke rike da kujerun siyasa wajen kada kuri’a a zaben shugabanni na kasa da za a gudanar ba.

The Cable ta ce wannan sanarwa ta fito ne a yammacin ranar Alhamis, 24 ga watan Maris 2022.

A wani jawabi da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa masu rike da mukaman gwamnati da aka zaba a matsayin masu kada kuri’a ba za su yi zabe ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel