Azumin Ramadan: Sarkin Musulmi ya yi gargadi kan kara farashin kayan masarufi

Azumin Ramadan: Sarkin Musulmi ya yi gargadi kan kara farashin kayan masarufi

  • Sarkin Musulmi ya jaddada kira ga gwamnati da yan kasuwa su tausayawa al'umma cikin watar Ramadana
  • Kayan masarufi na cigaba da hauhawa kulli yaumin kuma gashi watar azumi ta gabato, Sarkin ya fadi
  • Sarkin yace shugabanni su sani cewa an zabensu ne don kawowa al'umma sauki ba cika aljihansu ba

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, ya yi kira ga yan kasuwa suji tsoron ranar haduwarsu da Allah kada su kara farashin kayayyakin masarufi yayinda watar azumin Ramadana ke gabatowa.

Ya yi kira ga gwamnati ta san yadda zata rage farashin kayayyaki don rage zafin wahalar da mutane ke fama da shi.

Mai Alfarma Sarki ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar da taron rufe gasar musabaqar Alqur'ani ta kasa da akayi a jihar Bauchi, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Bayan zabtare albashin masu mukamai, hotunan shugaban kasar Ghana a Aso Rock sun bayyana

Azumin Ramadan
Azumin Ramadan: Sarkin Musulmi ya yi gargadi kan kara farashin kayan farashi
Asali: UGC

Yace:

"Ramadan na zuwa kuma tsadar rayuwa na kara karuwa. Ina son amfani da wannan dama don kira ga yan kasuwa suji tsoron abinda Allah zai yi musu ranar gobe qiyama idan suka hadu da shi."
"Maimakon kara farashin kayan masarufi da, ku taimaka ku rage farashin don samun albarkar Allah."
"Farashin kayan abinci ya tashi kuma yana cigaba da tashi, wajibi ne gwamnatoci magance wannan matsalar."

Sarki ya kara da cewa ranar Juma'a yana tare da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja kuma Limamin ya fadawa shugaban kasa wannan lamari.

Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron bude sabon Masallacin da kungiyar da'awa ta addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS ta gina a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Dan wasan Super Eagles, Shehu Abdullahi da jarumar Kannywood, Naja’atu, sun haifa yaro namiji

An bude Masallacin ne yau Juma'a, 25 ga Maris, 2022.

Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako na musamman a taron bude Masallacin.

Daga cikin wadanda suka halarci taron bude Masallacin akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan; Ministan birnn tarayya Abuja, Muhammad Bello; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar; da Kwamishanan ilimi na biyu na jihar Kano, Alaramma Ahmed Sulaiman, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel