Dan wasan Super Eagles, Shehu Abdullahi da jarumar Kannywood, Naja’atu, sun haifa yaro namiji

Dan wasan Super Eagles, Shehu Abdullahi da jarumar Kannywood, Naja’atu, sun haifa yaro namiji

  • Fitaccen dan wasan kwallon kafa na Super Eagles, Abdullahi Shehu, ya samu karuwar yaro namji daga matarsa jaruma Naja’atu Muhammad
  • Dan asalin jihar Sokoton mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Omonia dake Cypru, ya sanar da hakan a shafinsa na Instagram
  • Idan ba za mu manta ba, Shehu ya auri jarumar ne a wani bikin da ba a tara mutane ba da aka yi birnin Kanon dabo

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Abdullahi Shehu da matarsa, jarumar Kannywood, Naja’atu Muhammad Suleiman, sun haifa yaronsu na farko, da namiji.

Dan wasan mai shekaru 29, wanda a halin yanzu yana taka leda a kungiyar Omonia a Cyprus, ya sanar da wannan labarin mai dadi ne ta shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano

Dan wasan Super Eagles, Shehu Abdullahi da jarumar Kannywood, Naja’atu, sun haifa yaro namiji
Dan wasan Super Eagles, Shehu Abdullahi da jarumar Kannywood, Naja’atu, sun haifa yaro namiji Hoto daga @shehu.official
Asali: Instagram

A yayin da yake wallafa kyakyawan hotonsa tare da matarsa, mahaifin mai cike da farin ciki ya rubuta: “Mun yi farin cikin sanar da ku isowar ɗanmu, mahaifiyarsa da jaririn suna cikin koshin lafiya. Mun gode wa Allah!
“Muna farin ciki da wannan albarkar ta zuwan danmu a safiyar yau.
“Muna godiya da addu'o'in ku".

Asali: Legit.ng

Online view pixel