Karin bayani: Kotun koli ta tabbatar da batun soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa 22

Karin bayani: Kotun koli ta tabbatar da batun soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa 22

  • Kotun koli ta amince da matsayar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa
  • Soke rajistar da INEC ta yi a 2020 ya zo ne bayan da aka kammala zaben 2019, kuma jam'iyyun basu tabuka komai ba
  • Kotun koli ta ce, kotun daukaka kara ta yanke hukuncin watsi da umarnin INEC na soke rajistar wasu jam'iyyu 74

Abuja - Kotun koli a Najeriya ya tabbatar da hukuncin soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa 22 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi a shekarun baya.

Jam’iyyu 22 na daga cikin 74 da INEC ta soke rajistarsu a 2020 sakamakon rashin tabuka abin a zo a gani a zaben 2019, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta dage zaman shari'a kan sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC

Kotun koli kan batun soke rajistar jam'iyyun siyasa
Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da batun soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa 22 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Mai shari’a Ejembi Eko na kotun koli ya yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke, wanda ya kalubalanci matsayar INEC na soke rajistar jam'iyyun.

Mai shari’a Eko ya bayyana cewa, Kotun daukaka kara a karan kanta ta tabo batun rashin sauraron shari’ar adalci ga bangaren jam'iyyun 22 da aka soke, inda ta cimma matsaya ba tare da jin ta bakin wasu bangarori a kan lamarin ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar mai shari'a:

“Wannan bukata da INEC ta nema ya dace kuma an amince da hakan. Hukuncin kotun da ke kasa an yi watsi da shi.”

Kotun kolin ta bayyana cewa kotun daukaka kara ya fitar da batun sauraron karar ne daga duban bukatar daukaka kara da jam’iyyun siyasa suka shigar amma ta ki yin abin da ya dace domin yin adalci ga wasu da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Ramadan: Saudi ta ji uwar bari bayan ta nemi ta dakatar da haska sallolin dare da azumi

Jaridar Punch ta yi karin bayani da cewa, a ranar 6 ga Fabrairu, 2020, INEC ta soke rajistar jam’iyyun siyasa 74, saboda rashin samun nasarar lashe kujera ko daya na siyasa a babban zaben da ya gabata na 2019.

Yarjejeniyar takara: APC za ta shirya fitar da jerin sunayen hadin kai na taron gangami

A wani labarin, shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan jama’a na jam’iyyar APC mai mulki kuma gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule, ya ce a yau ne APC za ta shirya jerin sunayen hadin kan taron gangamin jam’iyyar na gobe Asabar.

Jaridar The Nation ta ce, Sule ya tabbatar da cewa tuni wasu shiyyoyin siyasar kasar nan suka amince da jerin sunayen da za a hada su a yau Juma'a.

Da yake jawabi a taron ganin babban taron gangamin da aka yi ranar Juma’a a Abuja, Sule ya kuma tabbatar da cewa tsarin yarjejeniyar ya kasance zabin farko na zaben sabbin shugabannin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Tsige Umahi: INEC Ta Ce Ba Za Ta Bawa PDP Kejurun Gwamna Da Ƴan Majalisun 16 Ba, Ta Bada Dalilli

Asali: Legit.ng

Online view pixel