An Maka Wata Tela A Gaban Kuliya Saboda Zargin Sayar Da Leshin Da Kwastoma Ta Kawo Mata Ɗinki

An Maka Wata Tela A Gaban Kuliya Saboda Zargin Sayar Da Leshin Da Kwastoma Ta Kawo Mata Ɗinki

  • Wata tela mai shekaru 33 ta gurfana gaban wata kotun majistare da ke Kaduna inda ake tuhumarta da siyar da leshin kwastomar ta
  • Leshin kamar yadda mai shi ta bayyana, ya kai tsadar N65,000, wanda telar ta musanta batun siyar da shi amma ta yi alkawarin biya
  • Kamar yadda mai gabatar da karar ya bayyana wa kotun, laifin ya ci karo da sashi na 339 da 321 na dokar Penal Code ta Jihar Kaduna

Kaduna - Wata tela, Lucy Jacob mai shekaru 33 tana fuskantar tuhuma a wata kotun majistare da ke garin Kaduna bisa zargin ta da siyar da leshin kwastoma mai kimar N65,000, Vanguard ta ruwaito.

Wacce ake zargin, tana zama ne a Sabon Tasha da ke Kaduna, kuma ana zarginta da cin amana da cuta, zargin da ta musanta.

Kara karanta wannan

Dan kuka: Mata za ta share harabar makarantar su danta na tsawon watanni 6 bisa laifin jibgar malami

An Gurfanar Da Wata Tela A Kotu Bisa Zarginta Da Siyar Da Leshin Da Kwastomanta Ta Kawo Mata Ɗinki
An maka tela a kotu bisa zarginta da siyar da leshin kwastomanta. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Mai gabatar da kara, Sifeta Chidi Leo ya sanar da kotu cewa mai karar, Ms Sarah Victor ta koka akan yadda ta kai wa wacce take kara leshin ta na N65,000 har shagonta a watan Disamba, amma telar ta siyar.

Mai gabatar da karar kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya zargi wacce ake karar da gaza cika alkawarin da ta dauka na biyan leshin a hankali.

Da farko ta amsa laifinta

Leo ya sanar da kotu cewa yayin da ‘yan sanda suke tuhumarta, wacce ake zargin ta amsa laifin ta akan cewa wata kwastomar daban ta siyar wa leshin.

Dan sanda ya ce laifin ya ci karo da sashi na 339 da 321 da dokar Penal Code ta Jihar Kaduna ta 2017.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari'a Ta Bada Umurnin a Tsare Wani Saboda Ɗunkulen 'Maggi' Katon 22

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya bayar da belinta a N100,000, sannan ya bukaci ta gabatar da tsayayyu biyu wadanda zasu nuna alamar biyan haraji.

Ya kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Mayun 2022.

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

A wani labarin da Legit.ng ta rahoto, wata kamfanin lauyoyi a Kaduna mai suna Moonlight Attorneys, a ranar Litinin, ta yi karar wani Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyan kudin N100,000 kudin aikin da suka masa.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Atiku Abdulra'uf, ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya nemi wanda ya shigar da karar ya yi masa aiki, kuma suka amince zai biya adadin a matsayin kudin aiki, rahoton Daily Nigerian.

Ya yi bayanin cewa bayan an kammala aikin, wanda aka yi karar ya ki biyan kudin duk da yarjejeniya da suka yi, hakan yasa wanda ya shigar da karar ya taho kotu don a bi masa hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel