Kano: Kotun Shari'a Ta Bada Umurnin a Tsare Wani Saboda Ɗunkulen 'Maggi' Katon 22

Kano: Kotun Shari'a Ta Bada Umurnin a Tsare Wani Saboda Ɗunkulen 'Maggi' Katon 22

  • Alkalin kotun shari'a a Jihar Kano ya bada umurnin a tsare masa wani Yusha'u Ado mai shekaru 37 a gidan gyaran hali
  • Hakan na zuwa ne bayan gurfanar da Ado da aka yi bisa batar katon din sinadarin dandano wato 'maggi' katon 22
  • Wanda ake zargin ya amsa laifinsa na batar sinadarin dandanon a hannunsa bayan ba shi amana ya ajiye wa wani

Jihar Kano - Wata kotun sharia da ke zamanta a Kano, a ranar Talata, ta tsare wani mutum mai shekara 37, Yusha'u Ado, bisa zargins da satar sinadarin dandano na abinci katon 22.

The Punch ta rahoto cewa Ado wanda yan sanda suka gurfanar da shi bisa laifin 'kutse da cin amana da cuta', ya amsa laifin da ake tuhumansa.

Kano: Kotun Shari'a Ta Bada Umurnin a Tsare Wani Saboda Ɗunkulen 'Maggi' Katon 22
Kotun Shari'a a Kano ta bada umurnin a tsare wani mutum saboda katon din sinadarin dandano guda 22. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Asalin yadda abin ya faru

Kara karanta wannan

Kwamitin bincike ya aike wa Abba Kyari sammaci, an sanar masa ranar gurfana

Dan sanda mai gabatar da kara, Abdullahi Wada, ya shaida wa kotu cewa, wanda ya shigar da karar, Jamilu Ibrahim, mazaunin Galadanci Quaters, Kano, ya yi korafi kan abin a ofishin Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar bayanan da yan sandan suka bada da farko, wanda ya yi karar ya kai korafi cewa ya bawa wani Ado ajiyar katon din sinadarin dandano katon 260.

Ya ce kudin katon din sinadarin dandanon, 22 ya kai N216,000, amma sai aka ce masa sun bata a lokacin da ya tafi ya karbi abinsa, rahoton The Punch.

Alkalin kotun, Dr Bello Khalid, ya bada umurnin cewa a tsare wanda ake zargin ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 18 ga watan Afrilun 2022.

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

Kara karanta wannan

Alkali ya iza keyar magidancin Bakano gidan yarin kan satar Maggi

A wani labarin da Legit.ng ta rahoto, wata kamfanin lauyoyi a Kaduna mai suna Moonlight Attorneys, a ranar Litinin, ta yi karar wani Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyan kudin N100,000 kudin aikin da suka masa.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Atiku Abdulra'uf, ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya nemi wanda ya shigar da karar ya yi masa aiki, kuma suka amince zai biya adadin a matsayin kudin aiki, rahoton Daily Nigerian.

Ya yi bayanin cewa bayan an kammala aikin, wanda aka yi karar ya ki biyan kudin duk da yarjejeniya da suka yi, hakan yasa wanda ya shigar da karar ya taho kotu don a bi masa hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel