Da alamun baraka a Kwankwasiyya yayinda wasu jiga-jiganta suka hadu da Sule Lamido

Da alamun baraka a Kwankwasiyya yayinda wasu jiga-jiganta suka hadu da Sule Lamido

  • Wasu jigogin jam'iyyar PDP sun yi kira ga uwar jam'iyya ta hukunta Sanata Kwankwaso bisa zargin Anti-Party
  • Wannan na faruwa ne yayinda jagoran jam'iyyar a Kano ke shirin sauya sheka daga jam'iyyar zuwa NNPP
  • Shugaban jam'iyyar PDP na bangaren Kwankwaso yace wadanda suka gana da Lamido jarkoki ne

Kano - Da alamun wasu jiga-jigan Kwankwasiyya a jihar Kano sun balle darikar yayinda suka yi zaman tattaunawa da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ranar Talata.

Daga cikin abubuwan da aka ruwaito sun tattauna kai shine kira ga uwar jam'iyyar PDP tayi watsi da jagoran darikar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, rahoton DailyTrust.

Kwankwaso, a makonnin da suka gabata ya kafa sabuwar kungiyar siyasa TNM kuma rahotanni sun nuna cewa yana kokarin sauya sheka jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Kara karanta wannan

Tsohon Mai magana da bakin Gwamna ya yi watsi da APC, ya bi NNPP ‘mai kayan marmari’

Sule Lamido
Da alamun baraka a Kwankwasiyya yayinda wasu jiga-jiganta suka hadu da Sule Lamido
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jiga-jigan Kwankwasiyya irinsu Dr. Adamu Dangwani, Yusuf Danbatta, Akilu Sani Indabawa, da wasu mambobin bangaren Ambasada Aminu Wali sun gana da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, a ofishinsa na Kano.

Mambobin Kwankwasiyyan a zaman suka cire jar hula.

A bayan zaman, jiga-jigan sun saki jawabin da akwai alamun Kwankwaso na son zama a PDP amma yana baiwa jam'iyyar NNPP karfi.

Danbatta wanda ya karanta Jawabin yace:

"Ana niyyar nakasa PDP a zaben 2023. Shirin shine hana PDP fitar da yan takara a zaben 2023 dubi ga tsarin sayan fam da jam'iyyar ta shirya."

Ya kara da cewa lokaci na kure musu tun da za'a rufe sayar da fam din takara ranar 1 ga Afrilu 2022, wanda idan ba dau matakin gaggawa, jam'iyyar PDP a jihar ba zata samu yan takara ba wanda hakan zai baiwa NNPP da sauran jam'iyyu cin zabe a bagas.

Kara karanta wannan

Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC

Amma Shehu Sagagi, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano wanda mamban kungiyar Kwankwasiya ne ya bayyana cewa wadanda suka hadu da Sule Lamido ba wasu jiga-jigai bane.

Ya ce tuni Lamdio na neman yadda zai yi tasiri a siyasar Kano amma ba zai samu nasara ba.

NNPP ta fara ratsa wasu jihohi, ta sha alwashin karbe mulki daga hannun APC da PDP

Jam’iyyar NNPP ta fito da sababbin shugabanni a jihar Nasarawa wadanda za su jagoranci jam’iyyar har zuwa 2026.

An fito da shugabannin ne ta hanyar maslaha a duka kananan hukumomi 13 da ke Nasarawa. Sababbin shugabannin sun ce za su karbe shugabanci a 2023.

Sabon shugaban NNPP na jihar ta Nasarawa, Sidi Bako ya shaidawa manema labarai cewa a shirye suke su kawo romon damukaradiyya ga jama’a a badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel