Tsohon Mai magana da bakin Gwamna ya yi watsi da APC, ya bi NNPP ‘mai kayan marmari’

Tsohon Mai magana da bakin Gwamna ya yi watsi da APC, ya bi NNPP ‘mai kayan marmari’

  • Tsohon Mai magana da yawun Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya fice daga jam’iyyar APC
  • Kwamred Bello Zaki ya bayyana shigarsa NNPP a lokacin da jam’iyyar tayi zaben shugabannin jiha
  • Akwai kusoshin APC da PDP da suka rike mukamai a Jigawa da suka sauya-sheka zuwa NNPP

Jigawa - A wani yunkuri na canza akalar siyasar Najeriya, jam’iyyar NNPP na cigaba da samun karin magoya baya a wasu jihohin Arewacin kasar nan.

Jaridar The Guardian a wani rahoto da ya fito a ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta samu karuwa a jihar Jigawa.

Hakan na zuwa ne bayan da shugabannin NNPP suka karbi wasu da suka canza shekar siyasarsu daga jam’iyyun APC da kuma PDP a ‘yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Da alamun baraka a Kwankwasiyya: Wasu jiga-jiganta sun ce a kori Madugu daga PDP

Rahoton ya ce tsohon mai magana da yawun bakin gwamnan jihar Jigawa, Kwamred Bello Zaki yana cikin wadanda suka shigo NNPP gabanin zaben 2023.

Sanata da Kwamishinoni sun shiga NNPP

Sanata Abdulaziz Tarabu yana cikin karuwar da jam’iyyar hamayya ta NNPP ta samu a Jigawa. Tarabu ya taba zuwa majalisar wakilai da na dattawa a PDP.

Ragowar wadanda suka sauya-sheka daga PDP zuwa wannan jam’iyya mai kayan marmari sun hada da wasu da suka rikewa Sule Lamido kwamishononi.

NNPP ‘mai kayan marmari’
'Yan jam'iyyar NNPP a Dutse Hoto: @MallamAminuIbrahim
Asali: Facebook

Tsofaffin kwamishinonin su ne Rabiu Isa Taura, Hannafi Fagam, da Shehu Chamo. Sai tsohon shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamna, Aminu Ringim.

Malam Aminu Ringim ya yi takarar gwamnan Jigawa a karkashin jam’iyyar PDP sau biyu a 2015 da 2019, duk ya sha kashi a hannun Alhaji Badaru Abubakar.

Kara karanta wannan

Bikin sauya sheka: Tashin hankali yayin da jiga-jigan PDP 70 suka sauya sheka zuwa APC

Bayan an karbi wadanda suka sauya shekan ne aka gudanar da zaben shugabanni inda jam’iyyar hamayyar ta fada hannun Hon. Mukhtari Ibrahim Gwanga.

Daily Post ta ce Zaki ya bayyana wannan matsaya da ya dauka ne a dandazon jama’a wajen zaben shugabanni na jiha da aka shirya a babban birnin na Dutse.

A cewar Zaki, dalilinsa na barin jam’iyyar mai mulki shi ne gazawar gwamnatin APC mai-ci.

NNPP ta yi zabe a jihohi

Dazu aka ji cewa 'Yan New Nigeria People’s Party su na cigaba da shirye-shiryen babban zaben 2023, an nada sababbin shugabanni a wasu jihohin kasar nan.

Umar Haruna Doguwa ne ya zama sabon shugaban NNPP a Kano, a Nasarawa kuma an zabi Sidi Bako yayin da Gambo Salisu ya zama shugaban NNPP a Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel