Allah ya karbi rayuwar ɗan kwamishinan Kwara awanni 24 bayan gama shagalin bikin ɗiyarsa

Allah ya karbi rayuwar ɗan kwamishinan Kwara awanni 24 bayan gama shagalin bikin ɗiyarsa

  • Allah ya yi wa ɗan tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kwara rasuwa awanni 24 bayan ya halarci bikin yar uwarsa a Ilorin
  • Tsohon kwamishina Musa Yeteti, ya nuna damuwarsa kan rashinsa, amma ya ce ya fawwala wa Allah komai
  • A cewarsa, wannan shi ne ɗan cikinsa na biyu da ya binne da hannunsa, bayan an masa jana'iza

Kwara - Tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kwara, Injiniya Musa Yeteti, ya yi rashin ɗaya daga cikin ƴaƴansa maza, Injiniya Nafi'u.

Mamacin ya rasa rayuwarsa da ƙarfe 11:00 na safe a Legas, bayan ya gaggauta kai kan shi Asibiti yayin da ya ji cikinsa na ciwo, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Matashin ɗan tsohon kwamishinan ya rasu ne awanni 24 bayan ya halarci bikin yar uwarsa a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

Musa Yeteti
Allah ya karbi rayuwar ɗan kwamishinan Kwara awanni 24 bayan gama shagalin bikin ɗiyarsa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wurin shagalin bikin ne, Mahaifinsu, wanda tsohon ɗan gani kashenin Bukola Saraki ne, ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Mamacin bai wuce shekara 28 a duniya ba, kuma tuni aka sallace shi kamar yadda Addini ya koyar kuma aka kai shi makwanci a maƙabartar musulmi dake Ilorin, ranar Talata.

Yadda lamarin ya faru lokaci ɗaya

Da yake jawabi, tsohon kwamishinan, wanda ya kira lamarin da abun baƙin ciki, ya ce wannan shi ne karo na biyu da ɗan cikinsa ya rasu.

A cewarsa:

"Ya bar Ilorin ranar Lahadi bayan gama biki domin ya koma Ofis ranar Litinin, kawai sai kira na samu daga matarsa, ta shaida mun baya jin daɗin jikinsa tun safe."
"Ya tuƙa kansa a Mota har zuwa Asibiti da ya fahimci ba shi da lafiya. Lokacin da matarsa taje Asibiti ta ga halin da ya shiga ne ta kira ni. Shekarunsa 28 kuma bai jima da samun ƴan biyu ba."

Kara karanta wannan

Rashin Wuta: Farashin Kalanzir ya yi tashin gwauron zabi, wahalhalu a Najeriya sun karu

"Na yi baƙin ciki amma na rungumi abin da Allah ya zartar. Shi ne ɗa na biyu da na binne, amma da ya rasu kafin bikin nan, da yanzu ba wannan labarin ake ba."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta gamu da babbar matsala, wani jigo tare da dandazon masoya sun koma PDP

Jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da wani cikas a Kwara yayin da take shirin babban gangamin taro na ƙasa ranar Asabar.

Tsohon ɗan takarar gwamna kuma jigo a APC ya jagoranci dandazon masoya sun koma jam'iyyar PDP mai hamayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel