Tsadar rayuwa: DSTv, GOTv za su kara kudin 'subscription' yayin da Ramadana ke karatowa

Tsadar rayuwa: DSTv, GOTv za su kara kudin 'subscription' yayin da Ramadana ke karatowa

  • 'Yan Najeriya su shirya ganin kari na kudi domin kallon tashoshin da ke kan tirken yada shirye-shirye ta DSTv da GoTV
  • A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, kamfanin na talabijin da sai an biya yake aiki ya bayyana cewa, sabon tsarin farashin zai fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu, 2022
  • Sabbin sauye-sauyen inji kamfanin na zuwa ne duba da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki tare da ganin hauhawar farashin kayayyaki, da kuma karuwar kudin man fetur

Wani rahoton jaridar Punch ya nuna alamar cewa, masu amfani da DSTv da GoTV a Najeriya za su fara biyan sabon farashi don kallon shirye-shirye a tashoshin da suka fi so, Multichoice ya sanar.

Sabon farashin wanda aka sanar wa jama'a a yau, Maris 22, 2022, kamfanin ya ce ya faru ne saboda hauhawar farashin kayayyaki da dawainiyar kasuwanci.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda

Karin kudin kallo a DSTV da GOTV
Tsadar rayuwa: DSTv, GOTv za su kara kudin kallon Tv gabanin Ramadana | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sabbin sauye-sauyen za su fara aiki ne daga Afrilu 1, kuma zai shafi dukkan tsarukan hulda na nau'ikan kamfanin guda biyu, rahoton PremuimTimes.

A cikin wata sanarwa da kamfanin na Mulichoice ya fitar a ranar Talata ya ce:

"Bisa la'akari da hauhawar farashin kayayyaki da dawainiyar kasuwanci, dole ne mu sake duba ga farashin kayayyakinmu don ci gaba da faranta wa abokan cinikinmu da nishadantar dasu a kowane lokaci da kuma ko'ina.
"Saboda haka, daga Afrilu 1, 2022, sabon tsarin farashi na bai daya a fakitin DSTV da GOtv za su fara aiki."

Sabon farashin DSTv

Multichoice ya ce yanzu fakitin DSTV zai zama kamar haka:

  1. Premium (N21,000)
  2. Compact + (N14,250)
  3. Compact (N9,000)
  4. Confam (N5,300)
  5. Yanga (N2,950)
  6. Padi (N2,150) )
  7. Business (N2,669)
  8. Xtraview + PVR (N2,900)

Kara karanta wannan

Kwastam Ta Kama Motar Ɗangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

Sabon farashin GoTv

Sabbin farashin fakitin GOtv zai zama kamar haka:

  1. Gotv Max (N4,150),
  2. GOtv Jolli (N2,800)
  3. GOtv Jinja (N1,900)
  4. GOtv Lite (N900)

Ya kara da cewa kwastomomin da suka biya kafin ranar cikar wa'adin (kafin 1 ga Afrilu, 2022) za su mori tsohon farashi, rahoton TheCable.

Hakazalika, Legit.ng Hausa ta fahimci, cewa karin na zuwa ne kwanaki kadan kafin shiga watan Ramadana; watan ilahirin musulman duniya, ciki har da 'yan Najeriya ke yawan sauraro da kallon wa'azukan addinin muslunci a cikinsa.

Kannywood: Bidiyon yadda wani Mutumi da ya karbi Musulunci saboda kallon Fim din Izzar So

A wani labarin, jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, kuma furodusan shirin 'Izzar So' mai dogon zango, Lawan Ahmad, ya ce wani bawan Allah ya karbi shahada sanadin kallon shirin.

Jarumin ya faɗi wannan kyakkyawan labari ne a wani sakon bidiyo da hotonsa da mutumin, wanda ya sanya a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

A cikin bidiyon, mutumin ya karɓi kalmar shahada wacce ke shigar da wanda ba musulmi ba zuwa cikin ni'imar musulunci, a kusa da jarumi Lawan Ahmad.

Asali: Legit.ng

Online view pixel