Zulum ya rabawa leburori 846 kudi N62m: Dattawa sun samu N100,000, matasa sun samu N50,000

Zulum ya rabawa leburori 846 kudi N62m: Dattawa sun samu N100,000, matasa sun samu N50,000

  • Zulum ya yiwa leburori masu aikin kwasan lodin kaya a Bolori Stores goma ta alkhairi ranar Litinin
  • Leburori sama da dari takwas sun samu kudi duba hamsin zuwa dubu dari don jan jari
  • Daya daga cikin leburorin wanda ke bayyana godiyarsa ga gwamnan yace wasu daga cikinsu basu taba rike kudi irin wannan ba

Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno a ranar Litinin ya raba kudi N62,750,000 ga dattawa masu aikin lebura a shagunan Bolori Stores dake Maiduguri.

Kowanne cikin Dattawa mutum 846 masu kwasan lodin kayan daga tirloli ne suka samu tallafin N100,000.

Zulum ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata a shafinsa na Facebook.

Gwamna Zulum
Zulum ya rabawa leburori 846 kudi N62m: Dattawa sun samu N100,000, matasa sun samu N50,000 Hoto: Governor of Borno State
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

IGP na ya sanda ya jinjinawa Sajen Yahaya da ya ki amsan cin hancin N300,000

Jawabin yace:

"Daga cikin mutum 846 da suka amfana, Zulum ya baiwa dattawa 409 wadanda suka dade suka aikin lebura a shagunan kudi N40.9 million."
"Hakazalika Gwamnan ya rabawa matasan leburori maza da mata 437 kudi N40.9 million inda kowanne ya samu N50,000."
"Zulum ya yi kira garesu suyi amfani da kudin wajen kasuwanci don kara samun kudin shiga."

Daya daga cikin leburorin wanda ke bayyana godiyarsa ga gwamnan yace wasu daga cikinsu basu taba rike kudi irin wannan ba.

Insha Allah zamu maida Magidanta 500 gidajen su, mu basu N100,000 su ja jari kafin Ramadan, Zulum

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, yace Magidanta yan gudun Hijira 500 daga Malam-Fatori, ƙaramar hukumar Abadam, za su yi azumin Ramadan a gida idan Allah ya so.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai wata ziyara yankin ranar Lahadi, kamar yadda gwamnatin Borno ta fitar a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Shin ka san wanene dan majalisar wakilan da yafi kowa dadewa a majalisa?

Tun a farkon faruwar matsalar ayyukan ta'addancin ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2014 mafi yawan mutanen garin Malam-Fatori suka bar gidajen su.

Yayin ziyarar da ya kai, gwamna Zulum ya duba gidajen wucin gadi 100 da magidantan ke amfani da su, kafin gwamnati ta kammala gyara musu gidajen su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel