Shin ka san wanene dan majalisar wakilan da yafi kowa dadewa a majalisa?

Shin ka san wanene dan majalisar wakilan da yafi kowa dadewa a majalisa?

Tun bayan dawowar demokradiyya Najeriya a shekarar 1999, daruruwan mutane sun wakilci al'ummar mazabunsu na tsawon shekaru, amma mutum guda kacal ya yi fice.

Majalisar wakilai na dauke da mambobin dari uku da sittin (360) kuma ana gudanar da sabon zabe bayan kowani shekaru hudu.

Yayinda wasu sukayi shekaru hudu amma basu samu daman komawa ba irinsu Hanarabul Farouq Adamu Aliyu, wasu sun yi shekaru takwas, wasu har 12.

Mutum guda ya kacal a tarihi ya samu nasarar lashe kowani zaben majalisa tun 1999 har ila yau.

Hanarabul Nicholas Ebomu Mutu zai cika shekaru 24 a majalisa idan ya kare wa'adinsa a 2023.

Mutu the Metusella
Shin ka san wanene dan majalisar wakilan da yafi kowa dadewa a majalisa?
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga abubuwan 4 da ya kamata ka sani game da shi:

Kara karanta wannan

Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne

1. Tun 1999 yake majalisar wakilan tarayya

2. Yana wakiltar mazabar Bomadi/Patani ta jihar Delta

3. Kowace majalisa, shi ake nadawa shugaban kwamitin NDDC

4. Bai taba fita daga jam'iyyar PDP

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Tun dawowar mulkin demokradiyya a Najeriya a shekarar 1999, akwai wasu mutane a kasar da suka shiga siyasar aka fara dama wa da su kuma har yanzu suna nan ba su gajiya ba.

Cikin irin wadanda sake dade a siyasar Najeriya suna amfana da kudin gwamnati saboda mukamai da dama da suka rike akwai irinsu Ike Ekweremadu, Ahmad Lawan, Danjuma Goje, David Mark da wasu.

A wannan rubutun, Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin wadannan yan siyasan da suka ka ga jiya kuma sun ga yau kuma da yiwuwar wasunsu za a cigaba da yi da su a gobe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Ga jerin sunayensu a nan:

https://hausa.legit.ng/siyasa/1459895-lawan-goje-amaechi-da-sauran-siyasa-4-da-ake-damawa-da-su-tun-1999/

Asali: Legit.ng

Online view pixel