Alkali ya iza keyar magidancin Bakano gidan yari kan satar Maggi

Alkali ya iza keyar magidancin Bakano gidan yari kan satar Maggi

  • Alkalin kotun shariar Musulunci da ke zama a Kano ya aike Yushau Ado gidan yari kan kama shi da laifin satar Maggi
  • An gano cewa wanda ya kai karar ya bashi ajiyar kwalayen Maggi a shagunansu amma da ya je dauka ya ga babu 22
  • Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi na cin amana da damfara, lamarin da yasa Alkali Bello ya aike da shi gidan maza

Kano - Wata kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai suna Yusha’u Ado mai shekaru 37 a gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin satar kwalayen Maggi da aka yi.

Wanda ake tuhumar mazaunin Goron Dutse Quarters Kano, yana fuskantar tuhuma guda biyu da suka hada da zamba cikin aminci da damfara, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Alkali ya iza keyar magidancin Bakano gidan yarin kan satar Maggi
Alkali ya iza keyar magidancin Bakano gidan yarin kan satar Maggi Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Sifeta Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da karar, Jamilu Ibrahim na Galandanci Quarters, ya kai kara ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Sifeta Wada ya ce wanda ya shigar da karar ya bayyana cewa, ya bai wa Ado kwalaye 260 na kayan dandano, wato Maggi da ya ajiye masa a shagonsa, kuma a lokacin da ya je daukar kayansa ya gano cewa kwalayen Maggin guda 22 da kudinsu ya kai N216,000 sun yi batan dabo.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, Daily Trust ta ruwaito.

Alkalin kotun, Dakta Bello Khalid, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Kano: Matashiyar budurwa mai shekaru 14 dake sana'ar saka tayils

A wani labari na daban, Fatima Saqibu Abubakar yarinya ce mai shekaru 14 a duniya mai zama a Ja’en kwatas a karamar Kumbotso ta jihar Kano.

Fatima tana aikin saka tayil a Kano, sana'a ce wacce aka san maza ke yin ta. Fatima ta sanarwa da Daily Trust cewa ta koyi aikin ne daga mahaifinta a shekaru kadan da suka gabata kuma tana zuwa makaranta.

Daily Trust ta bayyana cewa, a cewarta, ta fara karatun firamare a shekarar 2013 kuma yanzu haka tana aji hudu na sakandare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel