Kano: Matashiyar budurwa mai shekaru 14 dake sana'ar saka tayils

Kano: Matashiyar budurwa mai shekaru 14 dake sana'ar saka tayils

  • Fatima Saqibu Abubakar matashiyar budurwa ce mai shekaru 14 wacce ta fada sana'ar saka tayils gadan-gadan duk da maza aka fi sani da sana'ar
  • Matashiyar ta sanar da cewa ta koyi wannan sana'ar ne daga mahaifinta wanda kuma a halin yanzu tana ayyukan mutane
  • Ta sanar da cewa tana aji hudu na sakandare kuma tana fatan zama madubin da 'yan mata za su kalla su koyi wannan sana'a mai amfani

Kano - Fatima Saqibu Abubakar yarinya ce mai shekaru 14 a duniya mai zama a Ja’en kwatas a karamar Kumbotso ta jihar Kano.

Fatima tana aikin saka tayil a Kano, sana'a ce wacce aka san maza ke yin ta. Fatima ta sanarwa da Daily Trust cewa ta koyi aikin ne daga mahaifinta a shekaru kadan da suka gabata kuma tana zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Kasuwa Mazaunin Abuja Ya Shiga Jerin Masu Neman Gadon Kujerar Buhari a APC

Kano: Matashiyar budurwa mai shekaru 14 dake sana'ar saka Tiles
Kano: Matashiyar budurwa mai shekaru 14 dake sana'ar saka Tiles. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta bayyana cewa, a cewarta, ta fara karatun firamare a shekarar 2013 kuma yanzu haka tana aji hudu na sakandare.

"Shekaru kadan da suka gabata na fara aikin nan. Ina hango shi a matsayin mai matukar amfani gareni duk da ni mace ce. Ba zan yi zaman banza ko rashin aiki ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A gaskiya an fi ganin aikin saka tayil a matsayin aikin maza. Toh idan mace za ta iya koyon shi kuma ta kware, za ta zama dalilin da zai sa wasu yara matan sun koyi sana'ar domin dogaro da kai," tace.

A hankali tace ta fara ce wa mahaifinta ya bata dama ta gwada. Ya sha mamaki amma kuma ya bata dama.

"Ya hada min siminti kuma cike da mamaki ya ga na fara aiki me kyau. Daga nan na fara aiki da balallun tayils kuma a gida. Makwabta sun fara sani kuma suka fara bani aiki," tace.

Kara karanta wannan

A bidiyo mai taba zuciya, angon amaryar da aka birne ranar bikinsu yace ta ji a jikinta mutuwa za ta yi

Maula da ake tasa mu da ita yasa muke tserewa Abuja, mu sauya lambar waya, 'Yan majalisar Najeriya

A wani labari na daban, wasu 'yan majisar dattawa sun yi nuni da rushewar tattalin arzirki a matsayin dalilin bayyananniyar tazara tsakanin 'yan majalisa da mutanen su, inda suka kara da cewa magance matsalolin da ya shafi mutum shi kadai baya daga cikin dalilan da yasa aka zabe su.

Sun koka game da yadda basa iya gudanar da taro a dakin taron cikin anguwa hankali kwance ba tare da mutane sun bukaci a magance musu yunwar cikin su ba, inda suka kara bayyana yadda mutanen mazabar su suke son ganin an raba kudi a irin wannan taron.

Kamar yadda wani dan majalisa dake wakiltar mazabar Yalmatu Deba, Yunusa Abubakar, ya ce, dabi'ar maula da mutane ke wa 'yan majalisar ne yasa wasu daga cikin yan majalisar suka zabi zama a Abuja, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar

Asali: Legit.ng

Online view pixel