Sama da 70% na magungunan da ake amfani da su a Najeriya marasa inganci ne, NPHCDA

Sama da 70% na magungunan da ake amfani da su a Najeriya marasa inganci ne, NPHCDA

  • Hukumar kula da kananan asibitoci, NPHCDA, ta sanar da cewa kusan kashi sabain na magunguna da ake amfani da rabawa kasar nan jabu ne
  • Shugaban hukumar ya sanar da cewa yan Najeriya masu yawa ba su samun ingantacciyar hanyar samun kiwon lafiya
  • Ya ce rashin amfani da kananan asibitocin yasa jamaa ke tafiya na jihohi da na tarayya wanda hakan ke sake saka jamaa cikin talauci

Hukumar kula da kananan asibitoci ta kasa ta ce sama da kashi 70 na magungunan da ake amfani da su tare da rarrabe a Najeriya ba su da inganci.

Punch ta ruwaito cewa, hukumar ta kara da cewa mafi yawan ‘yan Najeriya ba su samun ingantacciyar kiwon lafiya.

Ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo ana dab da babban taron kula da kananan asibitoci mai taken: ‘Re-imaging Primary Health Care in Nigeria’.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mun dauki masu gadin al’umma 4200 don yaki da ‘yan ta'adda

Sama da 70% na magungunan da ake shigowa da su a Najeriya marasa inganci ne, NPHCDA
Sama da 70% na magungunan da ake shigowa da su a Najeriya marasa inganci ne, NPHCDA. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

A yadda hukumar tace, kasar nan ta na fuskantar kalubalen kiwon lafiya masu yawa, Punch ta ruwaito

Ya bayyana cewa, “Yawancin ‘yan Najeriya ba su samun ayyukan kiwon lafiya; Kashi 20 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu na faruwa a Najeriya; Yawan mace-macen jarirai na faruwa a adadin mutuwar 19 a cikin 1,000 da aka haihu; yara 'yan kasa da shekaru 5 na mutuwa a kan adadin 128 cikin 1,000; sama da kashi 70 na magungunan da ake bayarwa a Najeriya ba su da inganci.
“Tabarbarewa a tsarin PHC ya haifar da rashin amfani da PHC, wanda ya samar da nauyi mai yawa a cikin fannin kiwon lafiya, tare da majinyata kan dogara a kan ayyukan manyan asibitocin jihohi da na tarayya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu ta umarci AGF ya cire sashen da Buhari ya nema a cire daga dokar zabe

"Tsabar tsadar da ake fuskanta wurin samun ingataccen kiwon lafiya na sake kallafa bakin talauci kan jamaa"

Buhari ya sabunta nadin Faisal Shuaib a matsayin shugaban NPHCDA

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Dr Faisal Shu'aib a matsayin darektan hukumar habaka kananan cibiyoyin lafiya (NPHCDA) a karo na biyu, kuma na karshe.

Kamar yadda takardar da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yasa hannu a ranar 6 ga watan Oktoba, sabon nadin zai fara ne a ranar 10 ga watan Janairun 2020.

A wasikar, shugaban kasa ya taya Shu'aib murnar nada sa a karo na biyu, kuma yana masa fatan alkhairi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel