Buhari ya sabunta nadin Faisal Shuaib a matsayin shugaban NPHCDA

Buhari ya sabunta nadin Faisal Shuaib a matsayin shugaban NPHCDA

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Dr Faisal Shu'aib a matsayin shugaban NPHCDA

- Dr Shu'aib babban likita ne a BMGF dake Seattle a Amurika, kafin nadinsa na farko a Najeriya

- Ya jagoranci yaki da cututtuka masu hadarin gaske irin Ebola, Polio da sauransu, a Najeriya da Afirika

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Dr Faisal Shu'aib a matsayin darektan hukumar habaka kananan cibiyoyin lafiya (NPHCDA) a karo na biyu, kuma na karshe.

Kamar yadda takardar da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yasa hannu a ranar 6 ga watan Oktoba, sabon nadin zai fara ne a ranar 10 ga watan Janairun 2020.

A wasikar, shugaban kasa ya taya Shu'aib murnar nada sa a karo na biyu, kuma yana masa fatan alkhairi.

Dr Faisal Shu'aib, babban likita ne wanda ya kware a harkar lafiya kafin a yi masa nadi na farko a watan Janairun 2017, yayi aiki a matsayin babban ma'aikaci a BMGF dake Seattle a Amurika.

Dr Shu'aib ne ya jagoranci yaki da cutar Ebola a Najeriya lokacin da ta barke a 2014, a matsayinsa na shugaban yaki da cutar Ebola ta gaggawa.

Dr Shu'aib ya jagoranci yaki da cutar Polio a Najeriya da Afirika waddà WHO ta shirya a 25 ga watan Agustan shekarar 2020.

KU KARANTA: An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

Buhari ya sabunta nadin Faisal Shuaib a matsayin shugaban NPHCDA
Buhari ya sabunta nadin Faisal Shuaib a matsayin shugaban NPHCDA. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: El_rufai ya sanar da sabon Sarkin Zazzau

A wan labari na daban, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan yace za'ayi amfani da dokokin kare kai daga cutar COVID-19 a ranar Alhamis idan Buhari zai gabatar da kasafin kudaden 2021.

Yace da yawa daga cikin hadiman Buhari ba za su samu damar shiga majalisar ba. Duk wanda ke sha'awar ganin abubuwan da ke faruwa zai iya dubawa ta yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel