Kaakin majalisar Plateau da aka tsige ta bayan fagge ya fita daga APC, ya koma PDP

Kaakin majalisar Plateau da aka tsige ta bayan fagge ya fita daga APC, ya koma PDP

  • Tsohon kakakin majalisar jihar Filato ya koma jam'iyyar PDP daga APC bayan yaki da gwamnan jihar
  • An tsige Hanarabul Abok kwanakin baya ta bayan fagge kuma gwamnan ya wanke kansa daga lamarin
  • Dan majalisa mai wakiltan mazabar Jos ta gabas/Jos ta kudu an cire Ayuba Abok ne saboda fadar gaskiya

Kakakin majalisar dokokin jihar Plateau da aka tsige kwanakin baya Rt Hon Abok Ayuba a ranar Asabar ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC zuwa jam'iyyar People’s Democratic Party PDP.

Dan majalisan ya bayyana hakan a jawabin da mai magana da yawunsa, Samuel Kaze, ya saki.

Ya bayyana cewa ya mika takardar fita daga APC ranar 18 ga Maris don komawa jam'iyyarsa ta asali PDP a hedkwatar karamar hukumar Angware, gabashin Jos.

Kara karanta wannan

Sambo, Lawan, Gbajabiamila da wasu jiga-jigai sun dira Ilorin bikin diyar tsohon minista

Tsohon Kaakin majalisar Plateau
Kaakin majalisar Plateau da aka tsige ta bayan fagge ya fita daga APC, ya koma PDP
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

AIT ta ruwaito cewa ta samun tabbacin labarin daga bakin dan majalisan da kansa ranar Asabar a wayar tarho.

Abok yace ya yi hakan ne don ceton jihar Filato ddaga gajiyayyiyar gwamnatin APC a jihar.

Zaku tuna cewa yan majalisa takwas ciki ashirin da hudu suka tsige Kakakin Majalisa Abok ranar Alhamis, 28 ga Oktoba, 2021.

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato

Bayan tsigeshi, wasu jami’an tsaro suka kame tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar, Abok Ayuba da wasu ‘yan majalisa 10 da ke masa biyayya.

Da misalin karfe 3:15 na rana, kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Edward Ebuka, ya tasa ‘yan tawagar tsohon kakakin majalisar su 11 a motocin Hilux guda hudu.

Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa

Kara karanta wannan

Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu, dan majalisa

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Jos ta gabas/Jos ta kudu a majalisar dokokin tarayya, Dachung Bagos, ya yi zargin cewa ana hantarar tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Ayuba Abok ne saboda fadar gaskiya.

Bagos ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2021.

Ya ce an tsige kakakin majalisar ba bisa ka'ida ba domin shida daga cikin mambobin majalisar 24 ne suka aikata hakan, wanda a cewarsa ya yi kasa da kaso 2/3 da kundin tsarin mulki ke bukata don tsigewa.

Rahoton ya kuma ce Bagos ya kara da cewa an tsige kakakin majalisar ne ta karfi da yaji saboda ya fadi gaskiya a kan halin da tsaro ke ciki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel