Sambo, Lawan, Gbajabiamila da wasu jiga-jigai sun dira Ilorin bikin diyar tsohon minista

Sambo, Lawan, Gbajabiamila da wasu jiga-jigai sun dira Ilorin bikin diyar tsohon minista

  • Fitattun 'yan siyasan Najeriya duk sun halarci shagalin bikin diyar tsohon darakta janar na NILDS, Farfesa Abubakar Olanrewaju
  • Malamai masu tarin yawa sun yi wa'azi mai ratsa jiki ga ma'auratan inda suka hore su da zaman amana da hakuri
  • Daya daga cikin malaman ya yi kira ga shugabanni da su ji tsoron Allah wurin sauke nauyin da suka karba na shugabanci

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo; Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Ahmad Lawan; Kakakin majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila; sun kasance daga cikin manyan baki da suka hallara a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, domin halartar daurin auren Dr Aisha Abubakar Sulaiman, diyar Darakta Janar na Cibiyar Nazarin Dimokradiyya da Dokoki ta kasa (NILDS), Farfesa Abubakar Olanrewaju Sulaiman.

Kara karanta wannan

Kaakin majalisar Plateau da aka tsige ta bayan fagge ya fita daga APC, ya koma PDP

Gwamnan jihar Bauchi, Abdulkadir Bala Mohammed; mataimakin gwamnan jihar Kwara, Kayode Alabi; Ooni of Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi; da tsofaffin ministoci duk sun halarci bikin, Daily Trust ta ruwaito.

Sambo, Lawan, Gbajabiamila da wasu jiga-jigai sun dira Ilorin bikin diyar tsohon minista
Sambo, Lawan, Gbajabiamila da wasu jiga-jigai sun dira Ilorin bikin diyar tsohon minista. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Aisha ta auri Dr Hussain Kehinde Yahaya ne a wurin kayataccen biki wanda wakilin Ansarul-Islam Society of Nigeria na kasa Ustaz Hanafi Aara ya gudanar.

Sambo ya wakilci tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a wajen bikin.

A cikin hudubarsa, Aara ya bukaci sabon ango da ya bai wa matarsa kariya, ya kara da cewa dole ne ya tsaya tsayin daka a al'amuranta..

Malamin ya umurci ma'auratan da su sasanta tsakaninsu ba tare da barin wani ya ji kansu ba, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma gargadi ango da kada ya nisanta kanshi da amaryar domin dakile rugujewar aure.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan bayan shafe kwanaki ana duba lafiyarsa

A yayin da yake bayyana aure a matsayin abinda Allah ke kaddarawa a tsakanin musulmi masu imani, Aara ya yi kira ga ma’auratan da su nuna hakuri da juriya da takawa wajen mu’amala da juna.

A wani taron makamancin haka, Babban Mukadam na Ilorin, Sheik Suleiman Dan-Borno, ya gargadi masu rike da mukaman gwamnati da su yi kishi su kiyaye amanar da aka ba su a yayin gudanar da ayyukan ofisoshinsu.

Malamin ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a a wajen bikin walimah Al-Qur’ani da daurin auren Dr Aisha Abubakar Sulaiman, diyar Darakta Janar na Cibiyar Nazarin Dimokaradiyya da Dokoki ta kasa (NILDS), Farfesa Abubakar Olanrewaju Sulaiman, wanda ya gudana a Okeleru Family Quarters, Ilorin. .

Dan-Borno ya tunatar da masu rike da ofishin cewa lokaci ya kure da ake sa ran za su bar ofisoshinsu ba tare da la’akari da dadewar da suka yi ba.

Ya kalubalanci su da su sanya gaskiya da rikon amana su zama abin lura a kowane lokaci.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi kutun-kutun, aka tunbuke Sakataren APC kafin Mala Buni ya dawo daga Dubai

A irin wannan wa'azin, babban limamin garin Offa, Sheikh Muyideen Hussein, ya yi kira ga masu hannu da shuni a cikin al'umma da su taimaka wa marasa galihu, musamman ganin yadda watan Ramadan ke kara karatowa.

Babban Limamin Ilorin Sheikh Muhammad Bashir Soliu ne ya jagoranci zaman walima da addu’o’i ga amaryar.

Zafafan hotunan wankan da Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar Maishadda ta dauka a wurin bikinsa

A wani labari na daban, a yayin shagalin bikin Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da Hassana Muhammad, jarumai, mawaka da dukkan 'yan masana'antar sun samu halarta, hakan yasa aka yi bikin a fili domin dakin taro ba dole ya dauke su ba.

'Yan fim abokan sana'arsu sun matukar yi musu kara inda suka fito kwan su da kwarkwatarsu suka halarci bikin.

Manya irinsu Ali Nuhu, Rarara, Adam Zango duk sun halarta, kai hatta manyan mata irinsu Saratu Gidado, Hadizan Saima, Teema Makamashi duk sun samu halartar wurin bikin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kwamitin APC Na Riko Da Buni Ke Jagoranci Ta Sallami Sakatarenta, Ta Kada Kuri'ar Rashin Gamsuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel