Sokoto: Tankokin Mai Sun Yi Gobara a Kamfanin Simintin BUA, Ma'aikata 3 Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata

Sokoto: Tankokin Mai Sun Yi Gobara a Kamfanin Simintin BUA, Ma'aikata 3 Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata

  • Injiniyoyi uku a kamfanin simintin BUA da ke Jihar Sokoto sun rasa rayukan su a ranar Juma’a yayin da tankokin mai guda biyu suka fashe
  • An samu bayanai kan yadda wasu ma’aikata 3 suka ji raunuka wanda hakan ya ja aka zarce da su asibiti don a kula da lafiyar su
  • Majiyoyi sun bayyana yadda tankokin biyu suke cike da litocin mai miliyan biyar kafin wutar ta kama su, kuma lamarin ya faru ne na misalin karfe 9 na safe

Jihar Sokoto - Injiniyoyi 3 da ke aiki a kamfanin simintin BUA sun rasa rayukan su bayan tankokin mai guda biyu sun kama da wuta a Sokoto ranar Juma’a.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ma’aikata 3 suka ji raunuka sakamakon gobarar, hakan yasa aka zarce da su asibiti don kulawa da lafiyar su.

Kara karanta wannan

Ministan shari'a Malami: Ba zan yi murabus ba, sai na kammala wa'adin aiki na a mutunce

Sokoto: Tankokin Mai Sun Yi Gobara a Kamfanin Simintin BUA, Ma'aikata 3 Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata
Tankokin Mai Sun Yi Gobara a Kamfanin Simintin BUA a Sokoto, Ma'aikata 3 Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

An samu bayanai akan yadda daya daga cikin tankokin ke cike da Diesel yayin da dayar take cike da bakin mai.

Suna dauke da kusan lita miliyan 5 na mai

Wata majiya ta bayyana cewa tankokin suna dauke da kusan lita miliyan biyar na mai kafin ta kama da wuta.

Kamar yadda majiyar ta shaida, ma’aikatan suna tsaka da aiki a tankokin yayin da suka fashe da misalin karfe 9 na safe.

Fiye da sa’o’i 24 wutar tana ci gaba da babbaka bayan fashewar tankokin, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Wata majiya ta bayyana yadda wani bangare na ma’aikatan wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar ya babbake sakamakon tashin wutar.

An tattaro yadda tankokin suke kai wa sabuwar ma’aikatar diesel da bakin mai.

Kara karanta wannan

Ku cire ni daga bakinku: Maishadda bai yaudare ni ba, babu komai tsakaninmu – Aisha Humaira

Ana ci gaba da bincike akan sababin gobarar

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“Ina mai tabbatar muku hakan ba zai dakatar da ayyuka ba a ma’aikatar saboda akwai sauran wuraren da ake adana kayan aiki.”

Kakakin hukumar kwana-kwana na Jihar Sokoto, Bello Baban Addini ya ce yanzu haka suna kokarin kashe wutar.

Ya kula da cewa suna ci gaba da bincike don gano sababin gobarar, yawan wadanda suka raunana da kuma barnar da wutar ta yi wa ma’aikatar.

Har yanzu dai hukumar ma’aikatar bata ce komai ba dangane da lamarin.

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Kara karanta wannan

Ku barmu mu tara gashi: Shehu Sani ya kai ziyara ofishin Hisbah, ya mika bukatarsa

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel