Da Duminsa: Ƴan Bindiga Sun Jefa 'Bam' Cikin Ofishin Ƴan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 2, Sun Ƙona Motocci

Da Duminsa: Ƴan Bindiga Sun Jefa 'Bam' Cikin Ofishin Ƴan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 2, Sun Ƙona Motocci

  • Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a ofishin yan sanda da ke Umuguma a karamar hukumar Owerri West, Jihar Imo
  • Maharan sun toshe dukkan hanyoyin shiga ko fita da caji ofis din sannan suka jefa abubuwan fashewa ofishin ta kama da wuta
  • Bayan ofishin yan sandan ta kama da wuta, sun jira jami'an da ke cikin ofishin a waje inda suka bude musu wuta da bindiga suka kashe biyu

Imo - Yan sanda biyu sun mutu yayin da yan bindiga suka kona caji ofis a Umuguma a karamar hukumar Owerri West ta Jihar Imo, Rahoton Daily Trust.

Harin na zuwa ne awanni bayan mataimakin sufeta janar na yan sanda mai kula da zone 9, a Umuahia, Isaac Akinmoyede, ya bar jihar bayan ziyarar aiki na kwana daya.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun sace Likita daya tilo dake asibitin Gubio, jihar Borno

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Jefa 'Bam' Cikin Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kashe Jami'ai Biyu
'Yan Bindiga Sun Jefa 'Bam' Cikin Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 2. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Yadda maharan suka kaddamar da mummunan harin

An rahoto cewa a lokacin da maharan suka iso sun toshe hanyoyin shiga da fita ofishin yan sandan, har da wanda ke kusa da hedkatar karamar hukuma.

Daga bisani, sai suka kaddamar da hari ta hanyar jefa wasu irin abubuwa masu fashewa (bama-bamai) a cikin caji ofis din.

An gano cewa bayan cinna wa ofishin wuta, sun jira a waje domin kai wa yan sandan da suka fito daga ofishin hari.

Ganau ya bayyana cewa, yan sanda biyu da ke ciki sun fito inda maharan suka bude musu wuta.

An ce sunansu Ifeanyi da Iyke kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

An ce suna karatu a Jami'ar Jihar Imo da ke Owerri.

Ba a samu ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, Mike Abattam ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP, An Garzaya Da Shi Asibiti

'Yan Bindiga Sun Kona Gidan Shugaban Kungiyar Ohanaeze Indigbo Imo

A wani labarin duk a Imo, Yan bindiga, a ranar Asabar sun kona gidan shugaban kungiyar Ohanaeze Indigbo, Farfesa George Obiozor, a Awo-Omanma a karamar hukumar Oru East ta Jihar Imo.

The Punch ta tattaro cewa maharan sun isa gidan shugaban kungiyar na kabilar Igbo ne a motocci sannan suka jefa abubuwan fashewa cikin gidan.

An gano cewa Obiozor baya a gida a lokacin da aka kai harin.

Wata majiya ta ce:

"An kona gidan Farfesa George Obiozor a kauyensu. Na'urar dauka bidiyo na CCTV ta nadi yadda abin ya faru. Mun gode wa Allah Farfesan baya gida a lokacin da suka zo."

Asali: Legit.ng

Online view pixel