A bidiyo mai taba zuciya, angon amaryar da aka birne ranar bikinsu yace ta ji a jikinta mutuwa za ta yi

A bidiyo mai taba zuciya, angon amaryar da aka birne ranar bikinsu yace ta ji a jikinta mutuwa za ta yi

  • Wata matashiyar budurwa ta rasu ana saura kwanaki shagalin bikin aurenta, sannan aka birneta a ranar da ya kamata a yi shagalin bikinta
  • Marigayiyar amaryar, Mutoni Uwase Kenia, ta fuskanci matsanancin ciwo wanda yayi ajalinta a ranar Juma'a, 4 ga watan Maris, 2022 tana 'yar shekara 22
  • Sai dai mijinta, Jack ya bayyana yadda amaryar tasa ta hango mutuwar na karatowa, amma ta gaza karantar alamomin

A ranar da ya kamata a yi shagalin bikinta, wata matashiyar budurwa 'yar shekara 22, mai suna Mutoni Uwase Kenia aka yi bikin birne gawarta.

An birneta a ranar Juma'a, 3 ga watan Maris, 2022. Kenia ta bukaci sake ma ta aiki don bude ma ta mahaifa, amma hakan bai yuwu ba, saboda ita da mijinta basu iya biyan kudin yin aikin.

Kara karanta wannan

Bidiyon magidancin da ya gwangwaje matarsa da sabuwar mota a asibiti bayan ta haifa 'dansu na farko

A bidiyo mai taba zuciya, angon amaryar da aka birne ranar bikinsu yace ta ji a jikinta mutuwa za ta yi
A bidiyo mai taba zuciya, angon amaryar da aka birne ranar bikinsu yace ta ji a jikinta mutuwa za ta yi. Hoto daga Afrimax on YouTube
Asali: UGC

Afrimax ne suka wallafa yadda Kenia ta hadu da Jack Jack da labarin soyayyar su a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

Kamar yadda labarin ya nuna, masoyan biyu sun hadu ne a Facebook, yayin da wata rana suka hadu a zahiri.

Sai dai, Kenia ta sha mamakin ganin Jack, tsohon dan kwallon da shanyayyen barin jikinshi na dama a ranar da suka fara haduwa.

Duk da ya bayyana ma ta a Facebook cewa, bashi da lafiya amma ba tayi zaton ya tsananta haka ba.

Ta riga tayi nisa a soyayyarshi a soshiyal midiya, amma ta bar shi cikin takaici bayan gane hakan.

Daga bisani ta koma kulawa dashi, sannan ta zauna dashi na wasu satika. Dalilin hakan saboda baya iya hassala komi da kan shi.

Kara karanta wannan

Magidanci ya yasar da matarsa da 'ya'yansa a Najeriya, ya koma Spain da takardunsu

Afrimax ta bada labarin, inda masoyan suka samu kudin yin aurensu na coci daga tallafin da suka samu daga mutane.

Kenia da Jack basu da cikakkiyar lafiya

A lokacin da suke tsaka da shirye-shiryen shagalin bikin gida bayan auren kotu, Kenia ta fadi ciwo, inda aka garzaya da ita asibiti, a can ne likitoci suka gano yadda mahaifarta ke da matsalar toshewa.

Ma'auratan basu samu kudin yin aiki na biyu bayan na farkon da akayi, inda amaryar ta ce ga garinku ana saura kwanaki shagalin bikinsu na gida.

A jana'izar, mijin nata ya sha kuka. Jack ya bayyanawa Afrimax yadda matar tasa ta hango mutuwa na karato ta, amma ta gaza karantar alamomin.

"Ina tuna zaman mu na karshe ni da ita a gida. Ta rike ni da karfi, gami da sumbata na sosai, amma ba ta iya yin magana ba. A lokacin ne nayi kokarin garzayawa da ita asibiti.

Kara karanta wannan

Abin al'ajabi: Labarin Baturiyar da ta shekara 30 tana karantar da Hausa a Najeriya

"Ta nuna alamun tana so in juyo in kalle ta, amma ban fahimta ba.Alamu sun nuna yadda take fuskantar matsanancin ciwo," Jack ya fadi hakan ne cikin matsananciyar damuwa.

Jama'a sun yi martani

Ga wasu daga cikin tsokacin mutane da dama:

Bwalya ya ce: "Wannan labarin na da karya zuciya, na tuna lokacin na aka yi bikin, zuciya ta tayi dadi, kuma nayi musu murna, tana da zuciya mai kyau, sannan tana wa mijin so na gaskiya, Ubangiji ya bawa mijinta da danginsu hakurin jure wannan rashin, ki kwanta lafiya kyakyawa."
Christy Zesk cewa tayi: "Wannan labarin ya karya zuciya ta ta hanyoyi da dama.
"Naso a ce ina da damar sadaukar da wani abu don taimakawa, amma ni kaina ina hango lahira, kuma na kusa rasa matsugunni. Ba wai korona da ta zama sanadiyyar rasa aikina kadai ba, na kamu da cutar, kuma har yanzu ban dawo daidai ba tun lokacin.

Kara karanta wannan

Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar

"Duk da haka ba zan hakura da rayuwa ba! Na yi imani da yesu, gami da sa ran zai samar da abunda nake bukata don in rayu!
"Ubangiji yama wannan mutumin da dangin matarsa da abokananshi albarka. Ina roka musu kwanciyar hankali da farin ciki ya sake lullube zukatan su!"
Emmy Kanyembo ya ce: "Jack mutum ne mai karfin hali, kuma zai kalubalanci wannan matsalar. Ubangiji na nan, zai duba shi a lokutan tsanani.
"Labarin su ya cancanci jinjina saboda yana daya daga cikin labarin so da kulawa na hakika. Ubangiji ya jikan Kenia yasa tana cikin dausayin rahama. Wannan labarin na da girgiza zukata, kuma yana siffanta tsantsar soyayyar mutane biyu da suka shirye zama tare da tare da duban kalubale ba. Ina wa Jack fatan samun waraka cikin sauri."

Asali: Legit.ng

Online view pixel