Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji mafakar 'yan Boko Haram da ISWAP, sun ceto mutane 30

Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji mafakar 'yan Boko Haram da ISWAP, sun ceto mutane 30

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a wani yankin jihar Borno
  • Wannan lamari ya kai ga kwato makamai da kayayyakin aikin 'yan ta'addan inji rahotanni daga majiyoyi
  • Hakazalika, an ceto wasu mutane 30 da maharan suka sace a kwanakin bayan nan a wasu yankunan jihar

Borno - Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Desert Sanity sun ceto mutane 30 da wasu maharan Boko Haram/ISWAP suka yi garkuwa da su a jihar Borno.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a, an gano wadanda harin ya rutsa da su ne a wani samame da sojoji suka kai a kauyukan Ndufu da Musiri a jihar, Rahoton TheCable.

Boko Haram a jihar Borno
Sojoji sun ragargaji mafakar 'yan Boko Haram da ISWAP, sun ceto mutane 30 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

An kuma ce an kashe maharan da dama, yayin da aka lalata sansanoninsu daban-daban.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun dakile wani yunkuri na kai hari birnin tarayya

Wani bangare na sanarwar ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Jami’an tsaro sun kwato makamai tare da ceto mazauna yankin 30 da aka yi garkuwa da su.
“Bugu da kari, sojojin sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’adda daban-daban. Har yanzu ana ci gaba da aikin share fagen."

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suka ci ga da kai hare-hare kan 'yan ta'addan da kuma fafatawa tsakanin mayakan ISWAP da 'yan kungiyar Boko Haram.

Kimanin maharan tara ne rahotanni suka ce an kashe a ranar 8 ga watan Maris, lokacin da mayakan Boko Haram suka kaure da mayakan ISWAP a Borno.

Sa'o'i kadan kafin faruwar lamarin na ranar 8 ga watan Maris, sojojin Operation Hadin Kai sun kashe 'yan Boko Haram 17 a Damasak, karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.

A halin da ake ciki kuma, a ranar 16 ga Maris, an ce mayakan ISWAP sun yi garkuwa da Bulama Geidam, ma’aikacin lafiya a babban asibitin garin Gubio na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Rasha ta rasa 40% na Dakarun Sojojin da ta aika su aukawa mutanen Ukraine inji Jami’i

Rahoton TheCable ya ce 'yan ta'addan sun sace ma'aikacin lafiyan ne bayan da suka kai hari garin tare da kwashe kayan abinci da man fetur daga wata motar ma'aikatan jin kai.

Dubun wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika

A wani labarin, rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana cewa dakarunta sun yi ram da wani da ake zargin kasurgumin dan bindiga ne mai garkuwa da mutane, da wasu 26.

Rudunar yan sanda ta ce mutanen da suka shiga hannu suna daga cikin wadanda suka fitini mutane da kai harin garkuwa da fashi da makami, musamman a babbar hanyar Kaduna-Abuja.

A wata sanarwa da rundunar yan sandan Najeriya ta fitar ranar Alhamis da yamma a Twitter, kasurgumin dan bindigan dan kimanin shekara 36 ya amsa cewa shi ke jagorantar tawagarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel