'Karin Bayani: Allah Ya Yi Wa Babban Sarkin Gargajiya a Najeriya Rasuwa

'Karin Bayani: Allah Ya Yi Wa Babban Sarkin Gargajiya a Najeriya Rasuwa

  • Oba Moses Oyediran, shararren arkin gargajya na Jihar Osun, Ogunsua na Modakeke ya riga mu gidan gaskiya
  • Marigayi Oba Moses Oyediran ya rasu ne bayan shafe shekaru uku da 'yan watanni a kan gadon sarautar na Modakeke
  • Adegboyega Oyetola, gwamnan Jihar Osun ya mika sakon ta'aziyya ga al'ummar masarautar Modakeke bisa rasuwar sarkinsu mai adalci da son zaman lafiya

Jihar Osun - Shahararren sarkin gargajiya na Jihar Osun, Ogunsua na Modakeke, Oba Moses Oyediran, ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta rahoto.

Marigayin sarkin gargajiyan, dan asalin gidan sarautan Modakeke, ya zama sarki ne a shekarar 2018.

Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yi Wa Babban Sarkin Gargajiya a Najeriya Rasuwa
Allah Ya Yi Wa Babban Sarkin Gargajiya a Najeriya Rasuwa. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

Mazauna garin Modakeke sun ce an samu zaman lafiya a zamanin mulkin marigayin sarkin da cigaba sosai a garin na Modakeke.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Cikakken Jadawali: Chelsea zata barje gumi da Real Madrid da wasanni uku na Kwata-Final da aka haɗa yau

Sun bayyana cewa a zamanin sarkin ya tabbatar da zaman lafiya tsakanin garin da wasu garuruwa da ke kewayen su.

Gwamnan Jihar Osun ya yi ta'aziyar rasuwar Sarkin Modakeke, Oba Oyediran

Gwamna Adegboyega Oyetola na Jihar Osun ya mika sakon ta'aziya ga mutanen Modakeke bisa rasuwar sarkinsu.

A sanarwar da aka fitar a madadin gwamnatin jihar a ranar Juma'a, mai dauke da sa hannun kwamishinan labarai da wayar da kan al'umma, Funke Egbemode, ya bayyana Oba Oyediran a matsayin sarki mai tsoron Allah kuma mai hangen nesa da adalci.

Sanarwar ta ce:

"Gwamnatin Jihar Osun tana mika sakon ta'aziyya ga gidan saurata na Modakeke, Kwamitin Sarakunan Gargajiya da dukkan mutanen jihar bisa rasuwar Ogunsua na Modakeke, Oba Moses Oladejo Oyediran, Ajombadi III.
"Za a cigaba da tunawa da shi saboda tsare-tsarensa na cigaba, zaman lafiya da kaunar da ya ke yi wa mutanen Modakeke tsawon shekaru uku da yan kai da ya yi a mulki.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun sace Likita daya tilo dake asibitin Gubio, jihar Borno

"Duk da cewa sarautarsa gajeruwa ce, marigayi Ogunsua ya bar tarihi ya kuma yi wa mutanensa iya kokarinsa. Yana da niyyar ganin cigaban Modakeke, kuma a zamaninsa gwamnati ta yi wasu ayyukan cigaba da raya al'umma ciki da ginin hanyar Famia.
"Da aka yi yunkurin tada hankalin mutanen garinsa a shekarar bara, ta tashi ya yi tsayin daka ya kuma yi aiki da gwamnati don ganin an samu zaman lafiya a Modakeke."

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel