Amurka tayi magana a kan zargin cewa Hushpuppi ya tafka damfarar N165m daga kurkuku

Amurka tayi magana a kan zargin cewa Hushpuppi ya tafka damfarar N165m daga kurkuku

  • Babu gaskiya a zargin cewa Ramon Azeez ya sake tafka damfarar kimanin N165m daga dakin kurkuku
  • Gwamnatin kasar Amurka ta yi watsi da rade-radin da ake ji, haka zalika lauyoyin wannan mutumi
  • Wani malamin jami’a a kasar Amurka ya tabbatar da cewa labarin bogi ne kurum wasu suka kirkiro

United States - Ofishin babban lauyan gwamnatin kasar Amurka sun fito sun yi karin haske kan rade-radin da ke yawo a kan Abbas Ramon watau Hushpuppi.

Premium Times ta ce gwamnatin Amurka ta yi wannan bayani ne bayan an tuntube ta ta akwatin email.

Darektan harkokin yada labarai na ofishin babban lauyan kasar Amurka (da ke birnin Los Angeles), Thom Mrozek ya karyata zargin da ake yi wa Hushpuppi.

Mista Hushpuppi ya ce batun cewa Abbas Ramon ya saci $400,000 yayin da yake tsare a gidan yari ba gaskiya ba ne, jami’in ya ce wannan labari bai da wani tushe.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Hushpuppi ya sake tafka satar $400k a Amurka duk da yana hannun FBI

Kamar yada rahoton ya bayyana, tun da ya samu labarin, Thom Mrozek ya nuna shakkunsa, ya kuma yi alkawarin zai yi bincike domin ya gano gaskiyar zancen.

Labarin ba gaskiya ba ne

Da aka yi bincike mai zurfi, an fahimci cewa labarin da ya karade ko ina a ranar Alhamis ba gaskiya ba ne. Dama tun can labarin bai zo da cikakken bayanai ba.

Hushpuppi
Hushpuppi yana shanawa Hoto: Instagram / @hushpuppi
Asali: Instagram

Lauyoyin Hushpuppi wanda yanzu haka yake tsare a kasar Amurka sun nuna ba su san da wannan zance ba. Hakan ya kara nuna akwai kanshin rashin gaskiya.

A karshe Mrozek wanda shi ke magana da yawun babban lauyan gwamnatin Amurka a Los Angeles ya ce takardun da ake yawo da su a kan labarin na bogi ne.

Bayan an zurfafa bincike, gwamnatin Amurka ta karyata rahoton. Tribune ta ce Mrozek ya karyata labarin da ya zanta da manema labarai a yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya wawure na'urar buga takardu a Banki kan kin dawo masa da kudinsa

Bogi ce - Gary Warner

Wani kwarraren masani kuma malamin jami’a a kan harkar damfara ta yanar gizo, Gary Warner a shafinsa na Twitter ya ce labarin bogi ne wasu suka kirkira.

Mista Gary Warner ya ce wasu tsofaffin takardu aka yi wa kwaskwarima, ake yadawa da nufin Bayin Allah su ziyarci wani shafi na yanar gizo na ‘yan damfara.

Shari'a a Amurka

Tun a shekarar bara ku ka ji cewa mutumin da ake zargi da 419, Ramon Abbas, ya amsa laifuffukansa, ya yarda bai da gaskiya, a shari’ar da ake yi da shi.

Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi ya amince ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su nan satar kudi, damfara da dai sauransu a kotun kalifoniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel