Shahararren ‘Dan 419 a Duniya, Hushpuppi ya amsa laifinsa a kotu, zai tafi gidan yari

Shahararren ‘Dan 419 a Duniya, Hushpuppi ya amsa laifinsa a kotu, zai tafi gidan yari

  • Ramon Abbas ya hutar da Alkali, ya amsa laifuffukan da ake zarginsa da su
  • Hushpuppi na iya shafe shekaru 20 a gidan yari a dalilin laifuffukan da ya yi
  • Wannan mutumi ya yi kudi ne da damfar mutane, ta haka ya ba N160bn baya

Amurka – Mutumin da ake zargi da 419, Ramon Abbas, ya amsa laifuffukansa ya yarda bai da gaskiya, a shari’ar da ake yi da shi a Kalifoniya, Amurka.

Punch ta ce Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi ya amince ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su nan satar kudi, damfara da dai sauransu.

Kamar yadda takardun kotu suka nuna, Ramon Abbas ya tabbatar wa kotu cewa lallai bai da gaskiya.

Azeez watau Hushpuppi da kuma lauyansa, Loius Shapiro; da mukaddashin babban lauyan gwamnatin Amurka, Tracy Wilkison, sun sa hannu a takardar.

Rahoton ya bayyana cewa za a iya daure Hushpuppi na tsawon shekaru 20 a gidan yari a Amurka, tare da lafta masa tarar $500,000 (kusan Naira miliyan 260).

Kara karanta wannan

Amina ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari a dakinta, shi kuma ya nemi ta yi masa sabon aure

“Wanda ake tuhuma da laifin (Hushpuppi), ya yarda cewa ya aikata laifin da ake zarginsa da su, ya yarda cewa bai da gaskiya.”

Hushpuppi
Ramon Azeez, Hushpuppi
Asali: Instagram

Takardar ta ce daga Junairun 2019 zuwa Yunin 2020, wanda ake tuhuma ya hada kai da wani ko wasu, ya rika damfarar mutane a cikin Amurka da wajen kasar.

Wanda ake tuhuma ya san da cewa mafi tsaurin hukuncin da za a iya lafta wa duk wanda ya saba sashe na 1956(h) na dokar kasar Amurka shi ne daurin shekaru 20.

Za kuma a iya karbar kudin da suka ribanya asara ko ribar da mutum ya samu wajen wannan danyen aiki har sau biyu a matsayin hukuncin kama shi da laifin.

Hushpuppi ya na satar dukiyar jama'a ne daga bankuna, ta shafin yanar gizo da wasu dabarun zamani.

Daga wannan muguwar sana’a, ‘dan asalin Najeriyar ya tara kazamar dukiya, ya mallaki makudan kudi a bankuna da kuma manyan gidaje, da tulin motocin kece-raini.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na tsere daga Najeriya, na zo Benin – Igboho ya yi bayanin komai a kotu

Tarihin barnar Hushpuppi

Azeez mai shekara 37 ya fada hannun hukuma ne tun bayan da aka kama shi a birnin Dubai a shekarar 2020, daga nan ne aka mika shi ga FBI ta kasar Amurka.

‘Yan sandan Dubai suna zargin cewa wannan mutum ya damfari mutane 1,926,400 a kasashen Duniya abin da ya kai Dirham biliyan 1.6 (fiye da Naira biliyan 160)

Asali: Legit.ng

Online view pixel