Wani mutumi ya wawure na'urar buga takardu a Banki kan kin dawo masa da kudinsa

Wani mutumi ya wawure na'urar buga takardu a Banki kan kin dawo masa da kudinsa

  • Wani mutumi ya shiga banki a Najeriya, ya dauke na'urar buga takardu kuma yace dole a sauraresa
  • A bidiyon da ya bayyana, mutumin wanda ba'a bayyana sunansa ba yace bankin ta hanashi kudinsa
  • Yayinda yake kokarin fita daga bankin, mutane suka rika bashi hakuri kada yayi haka

Wani dan Najeriya ya dira cikin wani banki da rana tsaka ya dauke na'urar buga takardunsu saboda an ki sauraronsa.

An gi mutumin ne a wani bidiyo da ya yadu yana kokarin fita da na'urar amma mutane suka rokesa kada ya tafi.

Banki kan kin dawo masa da kudinsa
Wani mutumi ya wawure na'urar buga takardu a Banki kan kin dawo masa da kudinsa Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yana bin banki kudi

Bisa bayanin dake cikin bidiyo, mutumin ya yi ikirarin cewa yana bin bankin kudi kuma sun ki bashi tsawon watanni biyu yanzu.

Kara karanta wannan

Idan PDP bata ci zaben 2023 ba zata iya mutuwa gaba daya, Atiku

Yayinda ya bude kofar bankin zai fita, mutane suka rika bashi hakuri, sai ya tsaya yace:

"Shin zasu saurareni yanzu?"

Shafin Goosipmilltv ya daure bidiyon a shafin Instagram

Kalli bidiyon:

Martanin yan Najeriya kan lamari:

Gaddaf Man yace:

Yayi mistake kwarai dagaske muna Kara fada harakar Bank bata wuruwuru bace abi a hankali baza aci hakkin kaba saidai inkai kabari daukar doka da hannu YASABAMA shiri'a ta low and other

Ameenu Tukur:

Sunfi gane irin wannan yaren inshaallah hakan xai iya xama silar daina wulaqanta AL umma a banki

Usman T Janni:

Inama a garin mune Allah da sai na tayaka wannan rikicin dan nima 25k na har yau

Nazeef Nazee Bello:

Hakan yayi daedae KO ni xan iya yin haka idan raena ya baci a bank....sbd ma'ekatan banki Basu da mutunci sam

Abdullahi Katsina Muhammad:

Aikin banki fa ba ayi masa irin wannan abun, akan abinda bai kai ya kawo ba ya tadawa mutane hankali.

Kara karanta wannan

Mafarauta a jihar Borno sun kashe katon Zaki a garin Konduga

Lamarin kudi binsa akeyi a hankali Mtsewww

Abubakar Sani Ali:

Yayi daedae dan dasu ake hada baki ake satarwa mutane kudi

Usman Yunusa:

Banki yazama wahala ka ajiye kudi a gida barayi su dameka ka ajiye kudi a banki banki ma sata ga yahoo boys kayi yawo dasu a bugeka a kwace

Jamila Salisu:

Nima na fasa kaiwa court zanje nayi yanda nayi kawai ba sidi ba sadada sai naji cikin yar dari ta biyar sun zare hamsin dama sanyi Nike jira ya wuce saboda alkalin kada ya yanke hukunci da bashi bane

Asali: Legit.ng

Online view pixel