Babbar Magana: Hushpuppi ya sake tafka satar $400k a Amurka duk da yana hannun FBI

Babbar Magana: Hushpuppi ya sake tafka satar $400k a Amurka duk da yana hannun FBI

  • Dan son a sani a shafin Instagram Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi, an ruwaito yadda yake da hannu a wata badakalar damfara duk da yana gidan gyaran hali a Amurka
  • Wani jami'in FBI a Amurka ya shigar da sabon kara a kan Hushpuppi da laifin zamba da waskewa da kudade masu yawan gaske
  • Hushpuppi ya kasance a karkashin kulawar jami'an tsaro masu sanya sa ido a gidan gyaran hali na tsawon kwanaki bakwai yayin da aka ba shi damar yin amfani da intanet da kwamfuta

Rahotanni da ke fitowa daga waje sun tabbatar da cewa hukumar binciken manyan laifuka ta tarayya (FBI) a Amurka ta fitar da wasu sabbin tuhume-tuhume a kan dan damfarar dan Najeriya, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da HushPuppi.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa wani jami'in hukumar FBI a Amurka ya yi zargin cewa HushPuppi na da hannu a wani shirin waskiyar kudade da ya kai $400k a lokacin da yake tsare.

An mika wata takarda da ke tabbatar da wannan zargi zuwa Kotun Lardi na Amurka a ranar Laraba, 16 ga Maris.

Hushpuppi ya sake tafka sata
Babban Magana: Hushpuppi ya sake tafka satar $400k a Amurka duk yana hannun FBI | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kamar yadda yake kunshe a cikin takardar, an sake tuhumar HushPuppi game da sace kudi da zamba yayin da yake zaman jiran hukunci a gidan gyaran hali na Amurka.

An tattaro cewa yayin da yake gidan yari, ya gudanar da wata harkalla ta hanyar amfani da wasu katunan biyan kudi da aka samu daga bayanan waske kudaden ‘yan kasar Amurka da mazauna yankin.

Tsarin biyan kudi ta katin na Economic Impact Payments tallafin kudi ne da gwamnatin Amurka ke bayarwa ga mazauna Amurka bisa ga Dokar CARES.

Kara karanta wannan

Hush-Kyari: Ministan shari'a ya yi amai ya lashe, ya wanke Abba Kyari daga zargin damfara

Daya daga cikin hanyoyin da mazauna Amurka da suka cancanta suke karbar wannan tallafi na gwamnati ta hanyar amfani da katin Economic Impact Payments ne.

Yadda Hushpuppi ya wawure $429,800 daga gidan yarin Amurka

Takardar da aka kai kotu ta bayyana cewa, wasu 'yan damfara ta yanar gizo sun yi amfani da katikan na tallafin Amurka domin sayarwa wasu 'yan damfara a waje, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kamar yadda hukumomin Amurka suka tabbatar an ba Hushpuppi damar yin amfani da na'urar kwamfuta, wannan ya yi daidai da tanadin doka da ke bai wa fursunoni damar shiga wasu wuraren a takaitacciyar hanya.

An tattaro cewa an baiwa Hushpuppi damar yin amfani da intanet da kwamfuta tsakanin 28 ga Janairu zuwa 4 ga Maris, 2022 yayin da yake cikin gidan gyaran hali na Amurka.

An ce Hushpuppi yakan yi amfani da kwamfuta mai hade da intanet, inda ake zuba masa ido natsawon kwanaki 7 kacal.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

An gano cewa a cikin wannan lokacin, Hushpuppi ya sayi katunan zare kudi na EIP guda 58 da darajarsu ta haura $429,800 kuma ta nan ya wawure kudin ta hanyar wani wai shi AJ.

Hukumar NDLEA ta gano wasu Biliyoyin kudi kwance a cikin asusun Abba Kyari da yaronsa

A wani labarin, sababbin bayanai su na fitowa a game da tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda ta IRT, DCP Abba Kyari da kuma mataimakinsa, ACP Sunday Ubua.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa ana zargin wadannan jami’an ‘yan sanda biyu sun karbi Naira biliyan 4.2 lokacin da suke aiki kafin a ruguza tawagarsu.

Wannan yana cikin rahoton da NDLEA ta aikawa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel