Hukumar NDLEA ta gano wasu Biliyoyin kudi kwance a cikin asusun Abba Kyari da yaronsa

Hukumar NDLEA ta gano wasu Biliyoyin kudi kwance a cikin asusun Abba Kyari da yaronsa

  • Ana zargin DCP Abba Kyari da mataimakinsa, ACP Sunday Ubua da azurta kansu wajen aikin IRT
  • Binciken da jami’an NDLEA su ka gudanar ya tabbatar da cewa N4.2bn ya shiga asusun ‘yan sandan
  • NDLEA ta na tuhumar su Kyari ne da hannu wajen karbe tulin Tramadol da aka saida a kan N3bn

Abuja - Sababbin bayanai su na fitowa a game da tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda ta IRT, DCP Abba Kyari da kuma mataimakinsa, ACP Sunday Ubua.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa ana zargin wadannan jami’an ‘yan sanda biyu sun karbi Naira biliyan 4.2 lokacin da suke aiki kafin a ruguza tawagarsu.

Wannan yana cikin rahoton da NDLEA ta aikawa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da marigayi DIG Egbunike

Hukumar ta NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta ce akalla Naira biliyan 1.4 suka shiga asusun Kyari sa’ilin yana rike da IRT.

N2.8bn a asusun ACP Ubua

Shi kuwa mataimakinsa watau ACP Ubua ya karbi abin da ya zarce hakan. NDLEA ta ce an gano fiye da Naira biliyan 2.8 a wasu asusun bankinsa har takwas.

Binciken ya nuna cewa Sunday Ubua ya karbi N2.664bn a ranar 15 ga watan Agustan 2019. NDLEA ta na zargin wadannan kudi ne da aka samu daga saida kwayoyi.

Hukumar NDLEA
Dakarun NDLEA a kan aiki Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Cinikin Tramadol na N3bn

Kamar yadda jaridar ANN ta fitar da rahoto, hukumar ta na zargin cewa jami’an tsaron sun samu wannan biliyoyi wajen cinikin N3bn na kwayar Tramadol.

Wata majiya ta shaidawa ‘yan jarida cewa dama jami’an NDLEA su na binciken Kyari da mutanensa a kan zargin karbe tulin Tramadol a Odofin-Legas.

Kara karanta wannan

Yayin da yake Kasar Ingila, Buhari ya nada mukami, ya zabi sabon Shugaban HYPREP

Ana zargin dakarun IRT a karkashin jagorancin DCP Kyari sun dauke kwayoyin, sun saida a kasuwa. A lokacin nan ne asusun bankin Kyari da Ubua ya cika.

Daga cikin wannan kudi har N2.664bn da ACP Ubua ya samu, ya saye hannun jarin kusan N100m a wani banki. Legit.ng Hausa ba za ta iya kama sunan bankin ba.

A halin da ake ciki, NDLEA ta aikawa AGF takarda, ta na neman amincewarsa domin a karbe wasu kadarori da DCP Abba Kyari ya mallaka a fadin kasar nan.

Siyasar banga a Kano

Ku na da labari cewa kwanaki DSS ta taso manyan ‘yan siyasar Kano a gaba, har an tsare shugabannin kananan hukumomi biyu a dalilin rikicin APC.

Hukumar DSS ta yi wa AbdulSalam Abdulkarim Zaura, Baffa Baba Dan’gundi da Alhassan Ado Doguwa tambayoyi kafin a kira Murtala Garo shi ma ya yi jawabi.

Kara karanta wannan

Shiga aikin soja: Abubuwa 5 kuke bukata domin shiga aikin sojin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel