Musuluntar Da Ƙasar Ake Son Yi: Mabiya Addinin Gargajiya Sun Soki Halasta Saka Hijabi Ga Ƴan Sanda Mata

Musuluntar Da Ƙasar Ake Son Yi: Mabiya Addinin Gargajiya Sun Soki Halasta Saka Hijabi Ga Ƴan Sanda Mata

  • Kungiyar mabiya addinin gargajiya ta Najeriya, reshen Jihar Oyo, ta yi suka akan yadda gwamnati ta amince ‘yan sanda mata su dinga amfani da hijabi
  • Kungiyar ta yi sukar ne ta wata takarda wacce ta gabatar wa manema labarai a Ibadan wacce shugabanta, Surveyor Adefabi Dasola Fadiran da sakatarenta, suka sanya hannu
  • Sifeta Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba ya amince ‘yan sanda mata masu son amfani da hijabi su dinga sanyawa, wannan lamarin ya janyo surutai a kasar nan

Oyo - Kungiyar mabiya addinin gargajiya reshen Jihar Oyo, ta yi suka akan yadda gwamnatin Najeriya ta amince da amfani da hijabi ga ‘yan sanda mata da ke son amfani da shi, inda ta ce gwamnatin ta rasa inda zata mayar da hankali, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Goyi Bayan Dokar Hana Saka Hijabi a Indiya, Ta Ce Babu Addinin Da Ya Wajabta Saka Hijabin

Mabiya Addinin Gargajiya Sun Yi Suka Kan Amfani Da Hijabi Ga 'Yan Sanda Mata
Mabiya Addinin Gargajiya Sun Yi Suka Kan Halastawa 'Yan Sanda Mata Amfani Da Hijabi. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kamar yadda kungiyar tace ta wata takarda wacce ta gabatar wa manema labarai wacce shugaban kungiyar, Surveyor Dasola Fadiran da sakatrensa, Mogaji (Dr) Fakayode Fayemi Fatunde, suka sanya hannu, inda suka ce ana shirin mayar da kasar ta musulunci.

Sifeta Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, bai dade da amince wa ‘yan sanda mata sanya hijabi ba in har suna son hakan, wanda ya janyo surutai ta ko ina a kasar nan.

Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan muhimman matsaloli

Mabiya addinin gargajiyan kamar yadda Vanguard ta nuna, sun kara da cewa akwai matsalolin da kasa take fama da su musamman akan walwalar jami’an tsaro kamar ‘yan sanda da sojoji, yanayin ayyukan su da kuma samar da makamai masu kyau don yaki da ta’addanci, amma kuma hankalin shugabannin ‘yan sanda da gwamnatin yana kan hijabi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Bindige Mataimakin Shugaban Kungiyar Dilallan Katako a Borno

Kamar yadda takardar ta nuna:

“Alamu sun nuna cewa IGP ya daina boye shirin sa na mayar da Najeriya kasar musulunci. Akwai abubuwa da dama da suka yi wadanda bamu ce komai ba akai shiyasa suka ci gaba, har da sanya hijabi a kayan ‘yan sanda.
“Yanzu haka Najeriya tana fama da rashin tsaro, jami’an tsaron mu ba su da walwala kuma akwai sauran manyan matsaloli amma gwamnati ta mayar da hankali kan hijabi, wannan abin takaici ne.”

Idan ba a cire hijabi ba su ma mabiya addinin gargajiya zasu fara sanya kayan adon su

Kungiyar tana kira ga Buhari da Sifeta Janar na ‘yan sanda akan su yi gaggawar juya wannan batu su hana sanya hijabi idan ba haka ba mabiya addinin gargajiya zasu fara amfani da jigida, sarkar kafa da sauran kayan ado idan sun sanya kayan aikin.

Sun nemi gwamnati ta dakatar da batun hijabin saboda hakan zai iya kawo rashin jituwa da kuma rabuwar kawuna tsakanin mutane.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Tsohuwar Matar Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama A Kotu

Kamar yadda ya ce:

“Suna yawan cewa kasa daya, amma kuma halayyar su tana janyo rabuwar kawuna. Ya kamata shugabanni su dinga kokarin kawo hadin kai maimakon akasin hakan.
“Da haka suka janyo rikici a arewa bayan kawo dokokin yankuna wandanda suka janyo rashin yarda tsakanin yaruka daban-daban.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel