Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Bindige Mataimakin Shugaban Kungiyar Dilallan Katako a Borno

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Bindige Mataimakin Shugaban Kungiyar Dilallan Katako a Borno

  • ‘Yan bindiga sun harbe mataimakin shugaban kungiyar sarrafa katako da ke Jihar Borno, Mr Aga City har lahira kusa da anguwar su
  • Majiyoyi sun bayyana yadda suka harbe shi yayin da ya ke kokarin shiga motar sa kirar Corolla bayan yi wa iyalansa siyayya zai wuce gida
  • An yi gaggawar wucewa da shi asibiti mafi kusa da ke garin Maiduguri inda aka tabbatar ya mutu kamar yadda wani makusancin sa ya bayyana

Jihar Borno - Wasu ‘yan bindiga sun harbe mataimakin shugaban kungiyar sarrafa katako ta Jihar Borno, Mr Aga City, Vanguard ta ruwaito.

City, kamar yadda ake kiransa, dan asalin karamar hukumar Gwoza ne da ke cikin jihar.

'Yan Bindiga Sun Bindige Mataimakin Shugaban Kungiyar Dilallan Katako a Borno
Borno: 'Yan Bindiga Sun Bindige Mataimakin Shugaban Kungiyar Dilallan Katako. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Majiyoyi sun bayyana yadda marigayin yake zaune a Shagari low-cost kusa da Maimalari Cantonment a garin Maiduguri.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Yi Ƙarin Haske Kan Jitar-Jitar Cewa Ya Shiga Hannun Ƴan Bindiga

An harbe shi ne yayin da ya ke gab da shiga motar sa, kirar Corolla bayan ya siya wa iyalin sa taliya zai wuce gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani abokin mamacin wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya sanar da wakilin Vanguard cewa lamarin ya yi matukar firgita jama’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin

Kamar yadda ya shaida:

“An kira mu cikin gaggawa da dare yayin da aka shaida mana cewa da yammacin Alhamis an harbi abokin mu Mr Aga City a kusa da Shagari low-cost.
“An zarce da shi asibiti mafi kusa inda aka tabbatar ya rasu. Muna masa fatan samun rahama.”

Yayin tabbatar wa manema labarai ta sakon wayar salula, jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sanda, ASP Sani Shatambaya ya ce:

“Eh, rundunar ‘yan sanda ta sani kuma tana ci gaba da bincike akan lamarin.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 14 a Masallaci a Kaduna, Sun Kuma Sace Mata Da Dabobbi

A wani labarin, an sace wasu masallata a yayin da yan bindiga suka kai hari a masallaci a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun kai harin ne lokacin da mutanen ke sallar Ishai a ranar Alhamis.

Majiyar da ke zaune garin ya ce:

"Sun zagaye masallacin suka sace mutane 14. Sun kuma sace shanu da ba a san adadin su ba daga kauyen Tudun Amada duk a Giwa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel