Kotu Ta Goyi Bayan Dokar Hana Saka Hijabi a Indiya, Ta Ce Babu Addinin Da Ya Wajabta Saka Hijabin

Kotu Ta Goyi Bayan Dokar Hana Saka Hijabi a Indiya, Ta Ce Babu Addinin Da Ya Wajabta Saka Hijabin

  • A ranar Talata, babbar kotun Karnataka ta goyi bayan dokar haramta Hijabi a azuzuwa wanda gwamnatin kasar ta kallafa wa dalibai mata a makarantu
  • Alkalai uku na kotun sun bi bayan gwamnatin kasar na hana sanya hijabin inda suka yi fatali da karar da daruruwan daliban suka kai kotun
  • Wannan dokar ta yi matukar tayar da tarzoma a kasar, inda dalibai suka dinga zanga-zanga suna bukatar kada a tauye musu hakkin su a matsayin su na ‘yan kasa Indiya

Indiya - Wata babbar kotun Karnataka ta ce babu addinin da ya tilasta amfani da hijabi, yayin da ta bi bayan dokar da gwamnatin kasar ta sanya, The Punch ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan yadda wata kungiyar dalibai musulmai ta maka kara kotun inda suka dinga zanga-zanga tun shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Sunaye: Gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da jiha da za su iya rasa kujerunsu kan sauya sheka

Kotu Ta Goyi Bayan Dokar Hana Saka Hijabi a Indiya, Ta Ce Babu Addinin Da Ya Wajabta Saka Hijabin
Babu addinin da ya wajabta saka hijabi, In Ji Kotun Indiya. Hoto: Agency Report
Asali: Twitter

Kamar yadda alkalai ukun suka shaida ranar Talata:

“Mun bi bayan cewa sanya hijabin da mata musulmai suke yi ba wajibi bane a addinin musulunci.”

Kotun ta goyi bayan gwamnatin Indiya

Kamar yadda New Delhi Television ta ruwaito, gwamnatin Karnataka ta hana sanya duk wasu kaya da suka saba wa dokar gwamnati a makarantu da kwalejin ilimi a ranar 5 ga watan Fabrairu.

Kamar yadda The Punch ta nuna:

“Babu dalibin da zai kawo cikas ga kayan da makaranta ta tanadar. Gwamnati tana da damar bayar da doka wacce kowa zai bi.”

Babbar kotun Karnataka ta hana amfani da sutturun da addinai suka tanadar kamar hijabi da mayafai a watan da ya gabata, wanda hakan ya janyo dalibai suka dinga zanga-zanga, NDTV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

Wadanda suka kai karar daruruwan dalibai musulmai ne, sun sanar da kotu cewa hijabi hakkin bil’adama ne, kuma hana sanya shi kamar tauye hakkin ne. Amma kotun ta dakatar da wannan batu.

Tun farko gwamnatin ta hana sanya hijabin ne ga dalibai kadai banda malamai.

Tushen rikicin

Rikicin hijabin ya fara ne daga daliban wata makaranta Udupi da aka hana shiga aji saboda sun rufe kawunan su a karon farko cikin shekaru.

Yayin da dokar take ci gaba da zagaye makarantu, dalibai sun ci gaba da zanga-zanga sanye da mayafai, kamar yadda NDTV ta ruwaito.

Jam’iyyar Bharatiya Janata mai mulki ta bi bayan dokar inda ta nuna cewa babu wani addini da ya wajabta wa dalibai sanya wata suttura musamman hijabai.

Kamar yadda ministan harkokin majalisa da ma’adanai, Pralhad Joshi ya ce:

“Na bi bayan dokar kotun. Ina bai wa kowa hakuri kuma daga jiha har kasar nan duk sun ci gaba. Don haka muna bukatar kowa ya bi dokar"

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel