Gaba da gabanta: Alkalin kotun Abuja ya shiga jerin wadanda ake tuhuma da rashin da'a

Gaba da gabanta: Alkalin kotun Abuja ya shiga jerin wadanda ake tuhuma da rashin da'a

  • Majalisar shari’a ta kasa (NJC) ta dauki kwakkwaran mataki kan wasu alkalai biyu a Abuja da Kaduna
  • Mai shari’a Muawiyah Baba Idris na babbar kotun birnin tarayya Abuja ya shiga cikin jerin sunayen wadanda ake tuhuma da aikata rashin da'a
  • Shi ma wani alkalin kotun jihar Kaduna, Mohammed M. Ladan, ya samu gargadi daga hukumar ta NJC

Abuja - An sanya mai shari’a Muawiyah Baba Idris na babbar kotun birnin tarayya Abuja cikin jerin sunayen mutanen da ake tuhuma da aikata rashin da'a.

Kakakin hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC) Soji Oye ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an dauki matakin ne a taron majalisar karo na 97 a ranakun 15 ga Maris da 16 ga Maris, 2022.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraniya: An kashe yan jaridan Fox News biyu, an cirewa daya kafa

Alkali ya yi rashin da'a
Yanzu-Yanzu: Sunan alkalin kotun Abuja ya shiga jerin wadanda ake tuhuma da rashin da'a | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da NJC ta fitar ta shafinta na Twitter, wacce Legit.ng Hausa ta gano.

An gurfanar da Mai shari’a Idris ne bisa sanya hannu a kan wata takardar hukunci mai lamba FCT/HC/CV/FT/36/19 tsakanin Sicons Nigeria Ltd da Nile Place Restaurant and Catering Services Ltd.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar ta ce matakin ya saba wa tanadin doka mai lamba 27 (16) (b) ta Babbar Kotun Tarayya ta 2018 da kuma doka ta 4 (1) da (2) na dokar tilasta bin doka ta 2004.

An gargadi wani alkalin

Sanarwar ta kara da cewa, an ba wani alkali Mohammed M. Ladan na babbar kotun jihar Kaduna takardar gargadi.

Hukumar ta NJC ta ba Ladan takardar gargadi ne saboda wata shari'a mai lamba KDH/KAD/1321/2018 tsakanin VTLS Inc. da jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Kara karanta wannan

Bayan na jiya, wutar Najeriya ta sake lalacewa, Abuja, Legas, da wasu jihohin sun shafu

Hakazalika, a zaman an ba da shawarin nada alkalai 15 a matakin jiha da tarayya.

Aiki kai tsaye ga masu 1st Class: Majalisa ta tattauna kan daukar masu digiri aiki

A wani labarin, majalisar wakilai na son a fara daukar aiki kai tsaye ga daliban da suka kammala digiri da sakamako mafi kyau daga cibiyoyin ilimi na Najeriya, rahoton Channels Tv.

Majalisar ta yi imanin cewa hakan zai zama hanyar karfafa kwarin gwiwa ga daliban Najeriya da kuma baiwa wadanda suka kammala karatu damar kara kaimi a karatunsu.

Dan majalisar wakilai, Chinedu Martins, wanda ya gabatar da kudirin a ranar Laraba, ya ce hakan zai magance matsalolin ficewar daliban Najeriya masu hazaka daga kasar kamar yadda ake gani a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel