Kano: Kotu ta ba da umarnin a sake kwamushe tsohon kwamishinan Ganduje, Dan Sarauniya

Kano: Kotu ta ba da umarnin a sake kwamushe tsohon kwamishinan Ganduje, Dan Sarauniya

  • Kotu ta soke belin da ta ba tsohon kwamishinan ayyuka na Jihar Kano, Mu’azu Magaji
  • An soke belin ne saboda rashin bayyanarsa a gaban kotu har sau uku domin amsa tuhumar da ake masa na bata sunan Gwamna Abdullahi Ganduje
  • Kotun ta kuma yi umurnin kama Dan Sarauniya tare da mika sammaci ga mutane biyun da suka tsaya masa

Kano - Wata babbar kotun majistare ta soke belin da ta baiwa Mu’azu Magaji, tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, wanda ake tuhuma da bata sunan Gwamna Abdullahi Ganduje.

Kotun ta soke belin ne a ranar Litinin, 14 ga watan Maris kamar yadda jaridar PM News ta rahoto.

Kano: Kotu ba ba da umarnin a sake kwamushe tsohon kwamishinan Ganduje, Dan Sarauniya
Kano: Kotu ba ba da umarnin a sake kwamushe tsohon kwamishinan Ganduje, Dan Sarauniya Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A ranar 4 ga watan Fabrairu ne aka ba tsohon kwamishinan wanda aka fi sani da Dan Sarauniya beli a kan kudi naira miliyan 1 tare da mutane biyu da za su tsaya masa sannan kuma aka umarce shi da ya ajiye fasfo dinsa.

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

Bisa ga umurnin kotun, dole daya daga cikin mutanen da za su tsaya masa ya kasance hakimin kauyen Dan-Sarauniya a karamar hukumar Dawakin Tofa, sannan mutum na biyu ya kasance kwamandan Hisbah ko babban limamin kauyen Dan-Sarauniya.

Dalilin soke belin

Sai dai kuma, kotun karkashin jagorancin Mai shari’a, Aminu Gabari ta yanke wannan hukunci na soke belin kan rashin halartar zamanta har sau 3 domin amsa tuhumar da ake masa na bata sunan Ganduje.

Aminiya ta kuma rahoto cewa kotun ta bayar da umarnin kama Dan Sarauniya tare da mika sammaci ga mutane biyun da suka tsaya masa da su bayyana a kotun a ranar 28 ga Maris 2022.

Bayan kwana 2 da sakinsa, Mu'az Magaji ya ziyarci Shekarau, ya ce gwagwarmaya yanzu suka fara

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

A baya mun ji cewa kwanaki biyu bayan bada belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, wanda ya kasance a gidan yari kan zargin batawa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje suna, ya bayyana goyon bayansa ga tsagin Sanata Ibrahim Shekarau.

A wata ziyara ta musamman ga shugaban tsagin jam'iyya mai mulkin a gidan Sanata Shekarau, Magaji ya gana da Sha'aban Sharada, Danzago da wasu jiga-jigan jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Sai dai kuma, a wata tattaunawar gaggawa da manema labarai a gidan Shekarau a ranar Lahadi, Injiniya Magaji ya ce biyayyarsa yanzu ta koma wurin tsagin Shekarau saboda su ne suke yi wa Kano fatan alheri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel