An dauke wutan lantarki a duk Najeriya: Ministan Buhari ya kira taron gaggawa

An dauke wutan lantarki a duk Najeriya: Ministan Buhari ya kira taron gaggawa

  • Ministan Buhari ya shiga ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka samu baraka a wutar lantarki a yau Litinin, lamarin da ya tunzura 'yan kasar
  • Ministan ya bayyana manufar zaman, inda yace neman mafita aka zo ba daurawa wani laifi ba a yanzu

FCT, Abuja - Ministan wutar lantarki Engr. Abubakar D. Aliyu ya shiga ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki domin magance karancin wutar lantarki da ke haifar da matsalar dauke wuta a fadin kasar nan.

Daily Trust ta rahoto ministan yana gargadin cewa dole ne masu ruwa da tsaki su hada kai don ganin an samu mafita ga matsalar wuta.

Wutar lantarki ta dauki
An dauke wuta duk Najeriya: Ministan Buhari ya kira taron gaggawa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Taron wanda ya gudana a dakin taro na ma’aikatar wutan lantarki, ya samu halartar tawaga daga kamfanonin samar da wutan lantarki naTCN, NBET, NDPHC, NNPC, Shell da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Tserewa zai yi: NDLEA ta ki amincewa da bukatar belin Abba Kyari, an dage kara

A rahoton Vanguard da Legit.ng Hausa ta tattaro, ministan ya bude taron da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An kira wannan taro ne domin magance matsalar wutar lantarki a kasar nan da muke ganin ba a ji dadinsa ba.
“Dole ne mu nemo mafita ta yadda ‘yan Najeriya za su samu wutar lantarki. Ina so mu yi hakuri mu tattauna da juna, ba wai muna zargin junanmu ba”.

Aliyu ya ci gaba da cewa, gwamnatin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samu ci gaba a fannin samar da wutar lantarki ba kana da inganta samuwarsa a fadin kasar ba.

Ya kara da cewa dole ne a magance kalubalen da ake fuskanta.

A taron a cewar ministar, za a samar da hanyoyin da za su tabbatar da magance duk wasu matsalolin da suka shafi samar da wutar lantarki a Najeriya cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar

Manyan kayan abinci uku da farashin su ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar Legas

A wani labarin, abubuwan dake faruwa a fadin duniya na cigaba da shafar kayan masarufi a Najeriya, a cewar yan kasuwa.

A wani bincike da Legit.ng ta gudanar a wata babbar kasuwa a Najeriya, mun gano cewa farashin kayan abinci bashi da tabbas kuma samun su ya kara wahala.

Kamar Wake, Shinkafa da Gari, farashin ya sauka da sama da kashi biyar cikin dari yayin da kayan Masarufin da ake cikin kakarsu suka kara tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel