Yanzu-Yanzu: An Gano Ƙananan Yara Ƴan Shekaru 4 Da Aka Sace Cikin Wata Tsohuwar Mota

Yanzu-Yanzu: An Gano Ƙananan Yara Ƴan Shekaru 4 Da Aka Sace Cikin Wata Tsohuwar Mota

  • An gano kananan yaran nan yan shekara hudu, gano Wasiu Dauda da Al-Ameen Ibrahim da aka sace ranar Juma'a
  • An tsinci yaran biyu ne a yau Asabar cikin wata tsohuwar motar bas a babban titin Oshodi-Apapa a Legas
  • Mahaifyar Dauda, Mai suna Awau ta tabbatar da gano yaran inda ta ce a halin yanzu suna asibiti likitoci na duba su

Jihar Legas - An gano Wasiu Dauda da Al-Ameen Ibrahim, kananan yara yan shekaru hudu da aka sace a unguwar Ijesha da ke Legas.

Daily Trust ta rahoto cewa an gano yaran da ransu a cikin wata tsohuwar karamar motar bus a babban titin Oshodi-Apapa a safiyar yau.

Yanzu-Yanzu: An Gano Ƙananan Yara Ƴan Shekaru 4 Da Aka Sace Cikin Wata Tsohuwar Mota
An Gano Ƙananan Yara Ƴan Shekaru 4 Da Aka Sace a Legas. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An kuma sace kananan yara yan shekara 4 a Keke Napep bayan tashi daga makaranta

Mahaifiyar Dauda, Awau, ta shaidawa wakilin Daily Trust cewa a halin yanzu yaran suna can likitoci na basu kulawa a asibiti.

"Mun gano su. An tsince su a cikin wata tsohuwar karamar motar bus a kan babban titi a safiyar yau. Yanzu haka suna asibiti," a cewar mahaifiyar da ke cike da murna.

An gano kananan yaran sun bata ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma'a, awa biyu bayan sun dawo daga makaranta.

An ce wani mutum ne ya yi musu dabara ya basu biskit a lokacin da suke wasa ya shiga da su cikin adaidaita sahu ya tsere da su.

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep

A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin 'yan fim suna shagali a kamun Furodusa Maishadda da Jaruma Hassana Muh'd

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.

A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel