Magidanci Ya Roƙi Kotun Shari'ar Ta Umurci Tsohuwar Matarsa Ta Dawo Masa Da Sarƙar Zinarin Da Ya Bata

Magidanci Ya Roƙi Kotun Shari'ar Ta Umurci Tsohuwar Matarsa Ta Dawo Masa Da Sarƙar Zinarin Da Ya Bata

  • Mustapha Baba, wani dan kasuwa mazaunin Kaduna ya bukaci wata kotun shari'ar musulunci a jihar ta karbo masa sarkar zinari daga hannun matarsa
  • Matar, Amina Sani, wacce ta ce tana son mijin ya sake ta domin kada fushin Allah ya hau kanta don ba za ta iya masa biyayya ba, kuma ta ce ba za ta mayar masa sadakinsa ba
  • Lauyan wanda ya yi kara ya roki kotun ta dage sauraron shari'ar domin ba shi daman yin bincike da duba yiwuwar sulhunta ma'auratan ba tare da yawun kotu ba

Jihar Kaduna - Wani dan kasuwa, Mustapha Baba, a ranar Laraba ya roki wata kotun shari'ar musulunci da ke Jihar Kaduna, ta umurci matarsa da suke rikici, Amina Sani, ta dawo masa da sarkar zinari da ya bata.

Kara karanta wannan

Matata na neman halaka ni, na bata miliyan N2m ta ja jali ta salwantar da su, Miji ya nemi Kotu raba auren

Baba, wanda ke zaune a birnin Kaduna, ta bakin lauyansa, Ahmad Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa ya na da bukatu masu yawa, rahoton Daily Trust.

Magidanci Ya Roƙi Kotun Shari'ar Ta Umurci Tsohuwar Matarsa Ta Dawo Masa Da Sarkar Zinarin Da Ya Bata
Magidanci Ya Roƙi Kotun Shari'ar Musulunci Ta Umurci Tsohuwar Matarsa Ta Dawo Masa Da Sarkar Zinarin Da Ya Bata. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Tunda farko, matar Sani ta ce tana neman mijinta ya sake ta ne domin kada ta saba wa Allah ta hanyar dena yi wa mijinta biyayya.

Ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba zan biya miji na N50,000 da ya biya a matsayin sadaki ba domin ina son ya sake ni."

Lauyan wanda ya yi karar, MK Mustapha, ya roki kotun ta dage sauraron shari'ar domin ba shi daman yin bincike kan lamarin da kuma yiwuwar za su iya yin sulhu tsakanin mutanen biyu ba tare da kotu ta shiga tsakani ba.

Alkalin kotun, Malam Murtala Nasir, bayan sauraron bangarorin biyu ya ce a shari'ar musulunci, idan mata ta nemi a sake ta, za ta biya kudin sadakin da aka biya wurin aurenta.

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

Nasir ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Maris.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel