Matata na neman halaka ni, na bata miliyan N2m ta ja jali ta salwantar da su, Miji ya nemi Kotu ta raba auren

Matata na neman halaka ni, na bata miliyan N2m ta ja jali ta salwantar da su, Miji ya nemi Kotu ta raba auren

  • Wani magidanci dake zaune a birnin tarayya Abuja ya nemi Kotu ta ceci rayuwarsa daga hannun matarsa ta raba auren su
  • Mutumin ya shaida wa kotu cewa ya baiwa matarsa Miliyan N2m ta ja jali, ta kashe su kuma tana neman rayuwarsa
  • Matar wacce yar kasuwa ce ba ta halarci zaman Kotun ba, Alkali ya ɗage zaman zuwa ranar 24 ga watan Maris

Abuja - Wani ma'aikacin gwamnati, Ibe Kufu, ranar Alhamis ya roki Kotun Kostumare dake zamanta a Jikwoyi Abuja ta datse igiyoyin aurensa da matarsa.

Magidancin ya kafa hujjojin cewa matarsa ta salawantar da naira miliyan biyu da ya ɗauka a aljihunsa ya ba ta domin ta kama sana'a, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kotun Kostumare
Matata na neman halaka ni, na bata miliyan N2m ta ja jali ta salwantar da su, Miji ya nemi Kotu raba auren Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mutumin wanda ke zaune a babban birnin tarayya Abuja, shi ne ya zayyana wa Kotu haka a takardar shigar da ƙarar matarsa a gaban Kotun.

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

Daily Nigerian ta rahoto Ma'aikacin ya ce:

"Matata ba ruwanta da kulawa wajen kashe kuɗi, ta gaza tattalin kuɗin da na bata Naira miliyan biyu domin ta ja jali ta fara kasuwanci."

Magidancin ya kuma ƙara da shaida wa kotun cewa matarsa na neman ganin ta raba shi da rayuwarsa ta kowane hali.

"Matata na ta kokarin raba ni da numfashin duniya ta kowane hali. Ta faɗa mun lokuta da dama wata rana sai ta halaka ni."

Ya roki Kotun ta duba wannan lamurra ta datse auren su domin ceton rayuwarsa kuma ta ɗora alhakin kula da ƴaƴan da suka haifa a kan sa.

Shin matar ta amsa laifukan ta?

A nata bangaren, matar da ake ƙara mai suna Oma a taikaice, wacce take yar kasuwa, ba ta samu halartan Kotun ba.

Kara karanta wannan

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

Daga nan, Alkalin kotun, Mai Shari'a Labaran Gusau, ya ɗaga zaman zuwa ranar 24 ga watan Maris, 2022 domin cigaba da sauraron ƙarar.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Yan ta'adda da safiyar Alhamis, sun sake kai wani hari kauyen karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.

Rahoto ya tabbatar da cewa maharan sun kashe akalla mutum uku a Anguwar Galadima, sun yi awon gaba da wasu mata biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel