Innalillahi: Ɗa Ya Kashe Mahaifinsa Mai Shekaru 75 Da Duka, Ya Ce 'Wiwi' Ya Busa Ya Yi Tatil

Innalillahi: Ɗa Ya Kashe Mahaifinsa Mai Shekaru 75 Da Duka, Ya Ce 'Wiwi' Ya Busa Ya Yi Tatil

  • Yan sanda a Jihar Adamawa sun kama wani Nicodemus Ignatius bisa zarginsa da kashe mahaifinsa da suka
  • Ignatius ya amsa zargin da ake masa yana mai cewa ya sha taban wiwi ne kafin ya aikata amma ya yi nadama
  • Rahotanni sun nuna cewa tun a baya Ignatius ya taba barazanar kashe mahaifinsa, 'yan sanda suka kama shi amma mahaifin ya ciro shi

Adamawa - Yan sandan Jihar Adamawa sun kama wani mutum dan shekara 31, Nicodemus Ignatius kan zarginsa da kashe mahaifinsa mai shekara 75 da suka.

The Punch ta ruwaito cewa Nicodemus, dan asalin Unguwan Bistel a Song, karamar hukumar Song ya aikata abin ne a ranar 3 ga watan Maris, 2022, jim kadan bayan ya dawo daga mashaya.

Innalillahi: Ɗa Ya Kashe Mahaifinsa Mai Shekaru 75 Da Duka, Ya Ce 'Wiwi' Ya Busa Ya Yi Tatil
Innalillahi: Wani Ya Kashe Mahaifinsa Mai Shekaru 75 Da Duka, Ya Ce Wiwi Ya Sha. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

Tun a watan Nuwamban bara, Nicodemus ya taba yin barazanar cewa zai kashe mahaifinsa hakan yasa yan sanda suka kama shi. Amma saboda tausayi mahaifin ya saka aka ciro shi, rahoton Punch Metro.

Makwabcin su Nicodemus ya magantu kan lamarin

Wani makwabci, wanda ya yi magana da wakilin majiyar Legit.ng ya ce:

"Nicodemus ya dawo daga mashaya misalin karfe 8 na dare inda ya saba zuwa amma ya samu mahaifinsa da mahaifiyansa a daki sai ya rufe su.
"Amma, mahaifin dan shekaru 75, saboda tsoron dansa zai iya cinna wa gidan wuta, sai ya fito ta taga don ya tsere. Bai san dan yana nan labe da sanda ba.
"Wanda ake zargin, dauke da sanda, ya kama mahaifinsa da duka ya fasa masa kai hakan ya yi sanadin rasuwarsa."

Wanda ake zargin ya amsa ya kashe mahaifinsa, kuma ya ce wiwi ya sha

Bayan an kai rahoton wanda ake zargin wurin yan sanda, ya amsa cewa ya kashe mahaifinsa amma ya sha wiwi ne.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Nicodemus, wanda ya gaza bada wani takamamen dalilin kashe mahaifinsa ya ce:

"Na sha wiwi ne a ranar kuma na yi matukar nadamar abin da na aikata."

Martanin yan sanda kan lamarin

Kakakin yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce za a kai wanda ake zargin kotu nan ba da dade wa ba.

Ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da shi a kotu ya kuma gargadi mutane su guji daukan doka a hannunsu.

Saurayi ya kashe mahaifin budurwarsa ta hanyar daɓa masa wuƙa yayin da ya kama su suna 'soyewa' a gidansa

A wani labarin, An shiga ruɗani a Otu-Jeremi, hedkwatar ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu, Jihar Delta, a daren ranar Laraba, yayin da wani mutum ya daɓa wa mahaifin budurwarsa wuƙa, rahoton Vanguard.

An gano cewa rikicin ya samo asali ne bayan marigayin, wanda a lokacin haɗa wannan rahoton ba a ga sunansa ba ya dawo daga tafiya ya tarar da wanda ake zargin, Paul, yana soyewa da yarsa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Asali: Legit.ng

Online view pixel