Sojoji sun bindige wasu yan mata biyu har lahira bisa kuskure a kasuwar Kaduna

Sojoji sun bindige wasu yan mata biyu har lahira bisa kuskure a kasuwar Kaduna

  • Wasu sojojin Najeriya da suka ga bakin fulani a kan Mashin sun buɗe wuta a kasuwar Kidenda, karamar hukumar Giwa a Kaduna
  • Ba da nufi ba, harsasan sojojin suka yi ajalin wasu yan mata biyu har lahira, yayin da mutanen kasuwar ke gudun neman tsira
  • Mazauna yankin sun bayyana rashin jin daɗin su da lamarin, inda suka ce bai kamata sojojin su yi harbi cikin taron mutane ba

Kaduna - An samu tashin hankali a kauyen Kidenda, karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, lokacin da wasu sojoji suka yi ajalin wasu yan mata biyu har lahira a Kasuwa.

Wani shaidan gani da ido ya ce sojojin sun kutsa kasuwar ne a Mota yayin da suka ga wasu baƙi a kan Babura cikin kasuwar kuma suka kalubalance su, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Sojan Najeriya
Sojoji sun bindige wasu yan mata biyu har lahira bisa kuskure a kasuwar Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mutanen wurin suka fara guje-gujen neman tsira yayin da suka fara jiyo ƙarar harbin bindiga na tashi lokacin da sojojin suka buɗe wa baƙin mutanen wuta.

Matan da lamarin ya faru da su, Nurayn da Kahdija, suna kokarin neman mafaka ne yayin da harsasan soji ba da nufi ba suka yi ajalin su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban yayan yan matan biyu, Salisu Shuaibu Kidanda, ya bayyana cewa harsasan da sojojin suka harba cikin taron mutane ne ya yi ajalin yan uwansa.

Ya ce:

"Ko da fulanin da suka gani a kasuwan suka nufa meyasa zasu yi harbi cikin taron mutane? Yan uwana na kokarin gudu zuwa gida saboda kasuwar na wajen gari ne sai lamarin ya rutsa da su."
"Har yanzun sojojin ko ta'aziyya ba su zo mana ba kan abin da suka aikata, yan sanda ne kaɗai suka zo. Muna son a mana adalci saboda ba zaka kashe yan mata haka kawai ka yi gaba ba."

Wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa manema labarai cewa sojojin ba su da bukatar yin harbi a kasuwar domin Fulanin da suka harba tun farko sun tsere zuwa cikin jeji.

Me rundunar soji ta faɗa kan lamarin?

Da aka tuntubi mataimakin kakakin dakarun Division 1, Kanar Ezindu Idimah, ya ce an masa canji wurin aiki zuwa Abuja.

Ya umarci a nemi Laftanar Shehu, wanda har yanzun ba'a same shi ba domin jin ta bakin rundunar soji.

A wani labarin kuma Gwarazan yan sanda sun kama yan bindiga 200, yan fashi 20 a jihar Kaduna

Rundunar yan sanda ta jihar Kaduna tace ta samu nasarar yin ram da yan bindiga 200, yan fashi 20 a faɗin jihar.

Kakakin yan sandan ya kuma bayyana cewa hukumar ta kwato makamai da yawa duk a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel