Mallam Abba Gandu: Bakanon Da Ya Yi Shekaru 50 Yana Ciyar Da Zakuna Da Sauran Namun Daji a Zoo

Mallam Abba Gandu: Bakanon Da Ya Yi Shekaru 50 Yana Ciyar Da Zakuna Da Sauran Namun Daji a Zoo

  • Mallam Abba Gandu yana daga cikin wadanda suka fara aiki a gidan Zoo na Kano bayan kafa ta a shekarar 1971
  • Ya ce aikinsa shine ciyar da zakuna da sauran namun daji da ke gidan zoo din kuma yana matukar kaunar aikinsa
  • Mallam Abba ya ce ya shaku da dabobin sosai ta yadda duk inda ya ke yana tunaninsu sun zama tamkar cikin iyalansa

Kano - Tun shekarar 1971 da aka bude gidan Zoo na Kano don al'umma suka fara ziyara ne Mallam Abba Gandu dan shekaru 71 ya fara aiki a wurin.

Ya shaida wa BBC Pidgin cewa dabobin da ya ke ciyar da su fiye da shekaru 50 sun zama tamkar wani bangare na iyalansa.

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

Mallam Abba Gandu: Bakanon Da Ya Yi Shekaru 50 Yana Ciyar Da Zakuna Da Sauran Namun Daji a Zoo
Mallam Abba Gandu: Wannan sana'ar na ke son in cigaba da yi har in mutu. Hoto: BBC Pidgin
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na fara wannan aikin ne a 1971 bayan bude gidan Zoo saboda gonar mu ne ke wurin don haka bayan bude zoo din an dauki da dama cikinmu aiki."
"Na yi shekaru 50 a nan kuma aiki na shine ciyar da zakuna da sauran namun daji da ke zoo kuma ina matukar jin dadin aikin fiye da komai," in ji Abba.

Mallam Abba ya ce da wannan aikin ne ya gina gidansa shekaru da suka shude, ya yi aure sannan ya haifi yara takwas kuma duk suna zuwa makaranta, rahoton BBC Pidgin.

Mallam Abba ya yi bayanin yadda aikinsa ke kasancewa a kowane rana

"Na kan fara aiki ne misalin karfe 8 na safe idan na zo zan tafi in gabatar da kaina wurin mai gida na sannan daga nan in dauki naman da dabobi za su ci domin in raba musu.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki

"Kowane dabba yana da kasonsa bayan bayan na basu abincin na kan tsaya in kalli yadda za su ci, idan na ga wata matsala, zan sanar domin likitoci su zo su duba dabar."

Mallam Abba ya ce shi da dabobbin sun shaku

Ko da dare ne idan na zo kusa da zakunan suka ji kamshi na akwai wata irin kara da suke yi da ke nuna cewa sun san ni.

Mallam Abba ya ce ba shi da wani lokaci na musamman na tashi aiki domin aiki ne da ya ke kauna kuma ya shafe shekaru 35 yana yi don haka bai cika tashi da wuri ba.

"Da farko, bana aiki Asabar da Lahadi amma shekaru 35 da suka gabata, na fara aiki a kullum domin ba ni da wani abin da zan yi, duk ranar da ban zo ba yana nufin ban da lafiya.
"Ba zan iya wani aiki ba don wannan aikin na iya kuma na ke kauna. Dukkan zakuna 10 da ake da su a zoo tun 1971 har yau kamar yan uwa na ne kuma ina tuna su sosai, har wanda suka mutu," in ji shi.

Kara karanta wannan

Hotunan tsoho mai shekaru 79 da yayi shekaru 30 a daji yana rayuwa shi daya

Matasan zamanin yanzu dadi suke son ji ba aiki irin nawa ba, Mallam Abba

Daga karshe, kamar yadda BBC Pidgin ta rahoto, Mallam Abba ya ce yana fargabar kamar matasan da ya kamata su cigaba da aikin bayan ya dena ba za su so aikin ba.

"Matasan yanzu kawai jin dadi suke so, ba su son aiki irin nawa, wasu lokutan ina tunanin ta ina sabbin masu ciyar da zakunan za su fito."

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel