Yakin Rasha da Ukraine: Dangote ya shawarci FG kan matakin magance rashin abinci nan gaba kadan

Yakin Rasha da Ukraine: Dangote ya shawarci FG kan matakin magance rashin abinci nan gaba kadan

  • Aliko Dangote, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta hana saidawa kasashen ketare masara don gudun karancin ta saboda yakin Rasha da Ukraine
  • Da yuwuwar za a samu karancin abinci saboda Rasha da Ukraine sune manyan kasashen dake samar da sinadaran hada taki na fadin duniya
  • Dangote ya kara da cewa, yana fatan manoma za su zauna da gwamnati don yin garanbawul ga karancin abincin dake gabatowa

Aliko Dangote, shugaban kanfanonin Dangote ya bukaci gwamnatin tarayya ta hana Najeriya siyar wa kasashen ketare masara don gudun karancin ta sanadiyyar yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

Yayin martani ga tambayar da TheCable ta yi masa a taron karshen shekara na huda da kungiyar sarrafa abinci ta Najeriya ta shirya a ranar Alhamis, Dangote ya ce, Rasha da Ukraine sune manyan masu samar da sinadaran da ake amfani dasu wajen hada taki.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

Yakin Rasha da Ukraine: Dangote ya shawarci FG kan matakin magance rashin abinci nan gaba kadan
Yakin Rasha da Ukraine: Dangote ya shawarci FG kan matakin magance rashin abinci nan gaba kadan. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce, karancin wadannan sinadaran saboda yakin zai yi sanadin karancin taki da wasu kayayyakin abinci irin su; alkama da masara.

"Akwai yuwuwar za'a samu karancin alkama, masara da kayayyakin abinci da dama, saboda a yanzu da muke magana Rasha da Ukraine su ke samar da kusan kashi 30 cikin dari na sinadarin urea da kashi 26 cikin dari na sinadarin potash na fadin duniya- haka zalika sinadarin phosphate suna daya daga cikin manyan kasashe a duniya," a cewarsa.
"Da alama za a fuskanci karancin abinci a duniya, ba za mu samu damar samun taki ba, duk da ba za mu ga illar hakan yanzu ba, amma sai nan da watanni biyu zuwa uku. Saboda haka kasar Turai ba za su samu damar samar da amfanin gona kamar yadda suka samar a shekarar da ta gabata ba.

Kara karanta wannan

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

TheCable ta ruwaito cewa, Dangote ya ce, yana fatan manoma za su zauna da gwamnati don yin garanbawul ga karancin abincin da ke gabatowa.

"A halin yanzu, ya kai ga mutane suna siyar wa kasashen ketare masara don samun ribar kasuwancin kasa da kasa, wanda a ganina ya kamata mu dakata, don kada mu haifar da karancin abinci sannan ya kamata mu tabbatar da mun kara yawan noman mu, don gudun karancin abincin. Maganar nan a kan tsare abinci ne, kuma hakan abun lura ne matuka."

Muhimman lamurra 6 da ya dace a sani game da yakin Rasha da Ukraine bayan mako 2 da farawa

A wani labari na daban, a yayin da rikicin Rasha da Ukraine ya cika kwanaki 15, sojojin Rasha sun mamaye a kalla manyan birane hudu na kasar yayin da aka shirya birnin Kyiv domin ko ta kwana.

Har a yanzu babban birnin Ukraine na karkashin ikon kasa amma akwai yuwuwar Rasha ta kwace shi domin yadda take ta hararo shi, The punch ta ruwaito. Ga takaitattun al'amuran da ke faruwa ta kowanne bangare a yakin Rashan da Ukraine.

Kara karanta wannan

Buhari ya gwangwaje Afghanistan da tallafin $1m, OIC ta jinjina masa

Asali: Legit.ng

Online view pixel