Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya

Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya

  • Rahoton kasashe da suka fi fama da bakar talauci na shekarar 2022 ya nuna Najerya ta samu cigaba
  • Yanzu adadin yan Najeriya dake cikin matsanancin talauc ya sauko milyan saba'in
  • A ta'arifin majalisar dinkin duniya, duk wanda bai iya maganin N800-N900 a rana matalauci ne

Kasar Indiya ta zarcewa Najeriya a matsayin kasar da tafi adadin mutane masu fama da talauci a fadin duniya.

Wannan ya bayyana bisa rahoton da World Poverty Clock (WPC) ta saki na shekarar 2022.

World Poverty Clock (WPC) wani shafin yanar gizo ne dake bibiyan adadin mutanen da suke fadawa talauci kulli yaumin a kasashen duniya.

Majalisar dinkin duniya ta yi ta'rifin talauci a matsayin gazawar mutum ya samu $1.90 (N800) a rana.

Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya
Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya Hoto: https:/worldpoverty.io/map
Asali: Original

Kara karanta wannan

Tsabar kudi: Dangote ya tsallake matsayi mai girma, ya dara attajirai 429 da ake ji dasu a duniya

Bisa sabon rahoton WPC, yan kasar Indiya milyan 83 ne suka fada talauci a 2022, sabanin milyan 73 a shekarar 2018.

Najeriya kuwa itace ta biyu da adadin matalauta milyan 70, sabanin milyan 87 a shekarar 2018.

A 2020, hukumar lissafin Najeriya NBS tace sama da yan Najeriya milyan 80 ke fama da matsanancin talauci.

Na Gwammace In Biya N415,000 in Tafi Ukraine In Zama Bawa, Ɗan Najeriya Ya Yi Ɓaɓatu A Bidiyo

Wani mazaunin garin Abuja ya koka akan mawuyacin halin da Najeriya take ciki inda yace ya gwammaci ya biya $1,000 wato N415,000 a matsayin kudin jirgi don ya shiga cikin sojojin Ukraine maimakon ya tsaya a Najeriya.

Ofishin jakadancin Ukraine ta sakataren su na biyu, Bohdan Solty a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris ta bayyana yadda suka shirya tsaf wurin kwashe duk wasu ‘yan Najeriya da ke shirin tafiya kasar amma da sharadin kawo $1,000 don kudin jirgi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba rikicin APC ya damu talaka ba, yan jarida na batawa kansu lokaci kan rikicin APC, Buhari

Yayin tattaunawa da Legit TV inda aka yi masa tambayoyi, mutumin ya caccaki Buhari akan ba kasar Afghanistan $1m yayin da kungiyar malaman jami’a, ASUU take tsaka da yajin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel