Da Dumi-Dumi: Dandazon matafiya sun kwanta dama yayin da Tankar Fetur ta fashe kusa da MFM

Da Dumi-Dumi: Dandazon matafiya sun kwanta dama yayin da Tankar Fetur ta fashe kusa da MFM

  • Wani mummunan hatsari fiye da ɗaya da ya auku a wuri ɗaya ya lakume rayukan matafiyan dake kan hanyar da dama
  • Haɗarin wanda ya rutsa da motocin hawa biyu da kuma Tankar dakon man Fetur ya faru ne a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan
  • Kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa reshen jihar Ogun ta tabbatar da lamarin, ta kuma shawarci matafiya su bi a hankali

Lagos - Ana fargabar fasinjoji da yawa sun rasa rayuwarsu a wasu hatsarurruka na taho mu gama da suka faru akan babbar hanyar Legas-Ibadan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hatsarin ya rutsa da wasu motoci biyu da kuma Tankar dakon Man Fetur, suka ragargaje fiilla-filla a kusa da cocin MFM da ake kira birnin ibada.

Fashewar Tanka
Da Dumi-Dumi: Dandazon matafiya sun kwanta dama yayin da Tankar Fetur ta fashe kusa da MFM Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Babbar hanyar Legas zuwa Ibadan fitacciyar hanya ce da ta yi ƙaurin suna wajen yawan hatsarurruka domin daga shigowar wannan shekarar akalla mutum 30 suka rasa rayukan su.

Kara karanta wannan

Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya

Kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar aukuwar mummunan hatsarin ranar Talata a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Abeokuta.

Yadda lamarin ya faru a kan hanyar

Tribune Online ta rahoto Kakakin FRSC ɗin ta ce:

"Wani hatsari fiye da ɗaya da ya haɗa da babbar motar dakon Man fetur da Motoci biyu ya auku a kusa da Cocin Mountain Of Fire MFM dake kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan."
"An samu tashin wuta a wurin da haɗarin ya faru. Muna shawartan matafiya musamman direbobi su yi tuƙi cikin natsuwa da kula, har zuwa lokacin da za'a samu nasarar shawo kan wutar."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, sun kashe mutane su yi awon gaba da mata

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu zata fara zama kan bukatar FG na mika Abba Kyari kasar Amurka

Rahoto ya tabbatar da cewa maharan sun kashe akalla mutum uku a Anguwar Galadima, sun yi awon gaba da wasu mata biyu.

Wani mazaunin yankin ya ce sun jiyo karar harbin bindiga na tashi, kuma maharan sun aikata ta'addancin su ba tare da turjiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel