Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Hausawa Da Yarbawa Ƴan Kasuwa, An Ƙona Shaguna, Da Dama Sun Jikkata

Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Hausawa Da Yarbawa Ƴan Kasuwa, An Ƙona Shaguna, Da Dama Sun Jikkata

  • An samu bayanai akan yadda mutane da dama suka raunana a ranar Litinin da yamma bayan wani rikici ya barke tsakanin ‘yan kasuwa Yarabawa da Hausawa
  • Lamarin ya auku ne a kasuwar Lafenwa da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun wanda tun yammacin Litinin har safiyar Talata fadan bai kare ba
  • Bayan raunukan da mutane suka samu, an babbaka shaguna da dama wanda aka tafka asarorin miliyoyin nairori har sai da ‘yan sanda suka kai dauki

Ogun - Mutane da dama sun raunana a ranar Litinin da yamma bayan fada ya barke tsakanin ‘yan kasuwa Yarabawa da Hausawa a fitacciyar kasuwar Lafenwa da ke cikin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Majiyar The Punch ta tattaro bayanai akan yadda rikicin ya fara ruruwa tun yammacin Litinin har safiyar Talata wanda ya yi sanadiyyar babbaka shaguna da dama da kuma ji wa mutane da dama raunuka.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Hausawa Da Yarbawa Ƴan Kasuwa, An Ƙona Shaguna, Da Dama Sun Jikkata
Ogun: Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Hausawa Da Yarbawa Ƴan Kasuwa, An Ƙona Shaguna, Da Dama Sun Jikkata. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tushen fadan tsakanin yan kasuwan

Wata majiya ta shaida yadda asalin fadan ya fara daga wani Bayerabe da Bahaushe, kafin ya zama gagarumin rikici.

Majiyar wacce ‘yar kasuwa ce ta sanar da yadda aka ji wa wani Bahaushe mummunan rauni har ake tunanin ya kwanta dama, lamarin da ya harzuka Hausawan yankin inda suka lalata dukiyoyin miliyoyin nairori.

‘Yar kasuwar wacce ta bukaci a sakaya sunan ta, ta shaida cewa rikicin ya zama gagarumi ne bayan Sarkin Hausawan yankin ya yi kira akan a shiga cikin lamarin.

Kamar yadda majiyar ta shaida:

“An ji wa Sarkin Hausawan da ya yi kira akan kawo masalaha akan fadan mummunan rauni, hakan ya yi mutukar rura tarzomar.
“Yanzu haka yana asibitin tarayya da ke Idi-Aba, ana kulawa da lafiyarsa.”

Kakakin ‘yan sanda ya musanta batun rasa rayuka, ya ce babu wanda ya mutu

Kara karanta wannan

Kisan gilla kan Musulmai: Wani ya tashi bam a masallacin Juma'ah, mutum 56 sun rasu

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Ayeyemi, ya bayar da tabbaci akan aukuwar fadan.

A cewarsa, an kwantar da tarzomar. Oyeyemi ya shaida yadda rikicin bai yi ajalin kowa ba, ba kamar yadda aka dinga yada cewa an halaka wani Bahaushe ba.

Ya shaida yadda ‘yan sanda suka kama wadanda ake zargin suna da alaka da tayar da rikicin kamar yadda The Punch ta bayyana.

A cewar Oyeyemi:

“Na samu labarin rikicin amma an kwantar da tarzomar don mun kama wasu yanzu haka. Bana son in bayyyana yawan mutanen da aka kama, amma dai tabbas mun kama mutane.

“Sai dai ba gaskiya bane batun halaka rayuka, an dai tafka asarar dukiyoyi. Muna ci gaba da bincike akan silar tashin rikicin.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel